logo

HAUSA

Bai kamata a fake da batun tinkarar sauyin yanayi don neman cimma muradun siyasa ba

2021-04-18 21:48:30 CRI

Bai kamata a fake da batun tinkarar sauyin yanayi don neman cimma muradun siyasa ba_fororder_1

Kwanan nan ne a wajen taron kolin da aka yi ta kafar bidiyo tsakanin shugabannin kasashen Sin da Faransa da Jamus, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana muhimmin ra’ayinsa kan batun tinkarar sauyin yanayi, inda a cewarsa, tinkarar matsalar canjin yanayi, babban aiki ne a gaban daukacin bil’adama, kana, bai dace a fake da batun don neman cimma muradun siyasa a wani yanki ko kafa shinge a harkar kasuwanci ba. Haka kuma, bai kamata a yi amfani da batun tinkarar sauyin yanayi don sukar lamirin sauran kasashen duniya ba.

Wannan ra’ayi na shugaba Xi ya nuna babban kalubalen da ake fuskanta yayin da ake himmatuwa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi.

Bai kamata a fake da batun tinkarar sauyin yanayi don neman cimma muradun siyasa ba_fororder_2

Game da aniyar da gwamnatin kasar Japan ta yanke na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar tashar Fukushima a cikin teku, gwamnatin Amurka ta yi biris da ita, da zummar cimma muradunta a fannin siyasa.

Shugabannin Sin da Faransa da Jamus sun shaidawa duk duniya aniyarta, kuma a matsayin kasar dake bada shawarar kiran taron koli kan sauyin yanayin duniya tsakanin shugabannin kasa da kasa a makon dake tafe, ya dace Amurka ta nunawa duk duniya aniyar ta a fannin tinkarar sauyin yanayi, maimakon neman zama “jagora a fannin sauyin yanayi” bisa wannan hujja.(Murtala Zhang)