logo

HAUSA

Da gaske wasu ‘yan siyasar Japan sun kasa canja mummunar dabi’ar su?

2021-04-18 16:16:56 CRI

Da gaske wasu ‘yan siyasar Japan sun kasa canja mummunar dabi’ar su?_fororder_1

Kwanan nan ne, a wajen taron kolin kasashen Amurka da Japan, aka fitar da wata sanarwa mai jigon tinkarar kasar Sin, inda aka ambaci wasu muhimman batutuwan da suka shafi ikon mulki gami da babbar moriyar kasar Sin, ciki har da batun tekun gabashin kasar Sin, da tekun kudancin kasar, da Taiwan da Hong Kong da kuma Xinjiang, al’amarin da ya nuna cewa, ita kasar Japan tamkar baiwar Amurka ce.

Abun lura a nan shi ne, a cikin sanarwar da shugabannin kasashen Amurka da Japan suka fitar cikin hadin-gwiwa, wannan ne karon farko da aka shigar da batun yankin Taiwan a ciki. Duba da yadda Japan ta taba kutsa kai cikin kasar Sin gami da mulkin mallakar da ta yi a yankin Taiwan na kasar, babu shakka, wannan lamari zai haifar da mummunar illa ga dangantakar Sin da Japan.

Ana mamakin cewa, kasar Japan ta bayyana aniyarta na kyautata dangantaka tsakaninta da kasar Sin, amma ina dalilin da ya sa ta aikata haka yanzu? Ban da matsin lambar da ta fuskanta daga kasar Amurka, muradun da wasu ‘yan siyasar kasar suke kokarin neman cimmawa ya fi taka rawa. Wato, hana ci gaban kasar Sin bisa taimakon Amurka.

Da gaske wasu ‘yan siyasar Japan sun kasa canja mummunar dabi’ar su?_fororder_2

Bugu da kari, sakamakon gazawar gwamnati a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19, cutar a sabon zagaye ta sake bulla a kasar Japan. Haka kuma, tattalin arzikin kasar ya fuskanci mummunan koma-baya a shekara ta 2020. Ke nan, rashin bunkasa tattalin arziki gami da yaki da annobar COVID-19, ya sa gwamnatin firaministan kasar Suga Yoshihide ya bukaci a nemi wata dama don kwantar da hankalin al’umma, da samun goyon-baya a zaben shugabancin jam’iyyar LDP mai mulki a kasar wanda za’a gudanar a watan Satumbar bana. A dayan bangaren kuma, bayan da Joe Biden ya zama shugaban Amurka, gwamnatinsa tana maida kasar Sin a matsayin abokiyar karawar ta, abun da ya baiwa Japan babban zarafin da take bukata.

Ya dace wasu ‘yan siyasar kasar Japan su fahimci cewa, batun yankin Taiwan ya shafi babbar moriyar kasar Sin ne. Idan Japan ta ci gaba da hada kai tare da Amurka don kalubalantar kasar Sin a wannan fanni, babu shakka kasar Sin za ta maida martani sosai.

Shekara mai zuwa wato 2022, za a cika shekaru 50 da kafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Japan. Shin da gaske ne gwamnatin Suga Yoshihide a shirye take, wajen maraba da zuwan wannan muhimmiyar shekara ta hanyar yin ja-in-ja da kasar Sin?(Murtala Zhang)