logo

HAUSA

Wang Yu, mai wasan kayan kidan Sanxian na kasar Sin

2021-04-18 17:30:16 CRI

Wang Yu, mai wasan kayan kidan Sanxian na kasar Sin_fororder___172.100.100.3_temp_9500051_1_9500051_1_1_6123d3e1-cbdb-485c-8bd8-8843a6ecd528

Sanxian kayan kida na gargajiya na kasar Sin ne wanda ke da tsirkiya uku, wanda ake yawan yin amfani da shi musamman a wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar.

Wang Yu yana da shekaru 33 da haihuwa, kuma haifaffen birnin Beijing ne. Tun lokacin da yake dan shekaru 11 da haihuwa, malam Wang Yu ya fara koyon wasan kayan kida na Sanxian. Ya ce, "An haife ni a gidan masu wasan kide-kide. Kakana mai kidan Sanxian ne, baya ga haka kuma mahaifina da kawuna duka sun kasance masu aikin kidan Sanxian. A jikin bangon gidana, akwai nau’o’in kayayyakin kide-kide da ke makale."

Yanzu haka, malam Wang Yu ya kasance mai kidan Sanxian a kungiyar makada ta rediyon kasar Sin. Duk da haka, yana damuwa da yadda matasa masu shekarunsa ba su samu fahimta sosai dangane da Sanxian ba, har ma wasunsu ko sunan kayan kidan ma ba su sani ba. Don haka, yana fatan ganin karin mutane za su samu fahimtar kayan kidan da kuma nuna sha’awarsa. Ya ce,“Yanzu haka ban da wasan kidan Sanxian a cikin kungiyarmu, ina kuma dukufa a kan koyar da shi da kuma yin nazari a kansa, zan kuma wallafa wasu littattafai na koyarwa. A watan da ya gabata, na gama daukar wani hoton bidiyo na koyar da kidan Sanxian, wanda aka saka shi a shafin yanar gizo a kwanan baya. Ina yin wadannan ayyuka ne a kokarin kara tasirin Sanxian ga jama’a.”

A ganin malam Wang Yu, yadda ake ci gaba da amfani da Sanxian a yanzu baya ga tsawon tarihinsa na sama da shekaru dubu biyu ya nuna irin kyakkyawar rawar da kayan kidan ke takawa.“Kaka da kakaninmu sun ba mu nau’in kayan kida mai kyau haka, mu kuma nauyin da ke bisa wuyanmu ne mu kara yayata shi, don karin mutane su san shi.”

Baya ga haka, Wang Yu yana kuma wani kokari na ganin Sanxian yana tafiya tare da zamani, inda ya yi kokarin gyara kayan kida da kayayyaki iri daban daban, bayan da gwaje-gwaje da yawa da ya gudanar, a shekarar 2018, ya cimma nasarar kirkiro sabon nau’in Sanxian na zamani, ya ce,“A ganina, ya kamata a gaji al’adu tare da kara bunkasa su, a maimakon a ce a gaje shi ba tare da bunkasa ba, ko kuma a bunkasa shi amma ba tare da gadon nagartar al’adun ba.”