logo

HAUSA

Sanawar Amurka kan yankin Hong Kong za ta taimakawa masu barna wajen kara aikata laifuka

2021-04-18 17:20:54 CRI

Sanawar Amurka kan yankin Hong Kong za ta taimakawa masu barna wajen kara aikata laifuka_fororder_1

Kwanan nan ne Amurka ta fitar da wata sanarwa, inda ta nuna yatsa ga wani hukunci mai adalci da kotun yankin Hong Kong na kasar Sin ta yanke, kan wasu masu tada kayar-baya a yankin, inda ta bukaci kasar Sin ta saki wadanda suka aikata munanan laifuka babu gaira babu dalili.

Sanarwar Amurka ta bayyana Jimmy Lai, da Martin Lee gami da Albert Ho a matsayin wai “jagororin masu gwagwarmayar tabbatar da demokaradiyya”, amma hakikanin gaskiya, su ne masu barnata tsarin demokuradiyya a Hong Kong. “Taron gangamin neman zaman lafiya” da suka halarta ko kuma jagoranta, gangami ne da aka yi ba bisa doka ba wanda ya haifar da tashe-tashen hankali a Hong Kong, da kawowa kasar Sin baraka.

Sanawar Amurka kan yankin Hong Kong za ta taimakawa masu barna wajen kara aikata laifuka_fororder_2

Hukuncin da kotun Hong Kong ta yankewa wadannan masu barna a wannan karo, ya shaida cewa Hong Hong wuri ne mai mutunta doka da oda, kana ya biya bukatun al’ummar yankin.

Zaman lafiya, da demokuradiyya, da ‘yanci, muradun daukacin al’umma ne a duniya. Ya dace duk duniya ta bayyana ainihin ma’anar su ba Amurka ita kadai ba. Hakikanin gaskiya, akasarin kasashe ba su amince da muradun Amurka a matsayin muradun kasa da kasa ba, kana, ka’idojin Amurka ba ka’idojin kasa da kasa ba ne.(Murtala Zhang)