logo

HAUSA

Gaskiyar “aikin tilas”

2021-04-18 21:46:56 CRI

Gaskiyar “aikin tilas”_fororder_d439b6003af33a87043d549614d22d305243b505

“Ina samun kudin da ya kai yuan dubu 4000 a nan wajen a kowane wata, a yayin da mai gidana yana samu sama da 5000, wato gaba daya sama da 9000 ne muke samu, albashin da muke gamsuwa da shi. Rayuwata ta inganta kwarai bayan da muka fita cin rani a nan, har muka sayi gidan da ya kai fadin mita 87 a garinmu, wanda muka biya kudin yuan fiye da dubu 200……” Wata ‘yar cin rani da ta fito daga gundumar Akqi ta jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin ce ta fadi haka a yayin tattaunawar da ta yi tare da marubutan wani rahoto mai taken “Aikin tilas ne ko kuma neman ingantuwar rayuwa? Bincike dangane da yanayin ‘yan cin rani na jihar Xinjiang”, rahoton da jami’ar Jinan ta fitar a kwanan baya.

Wannan ‘yar cin rani da aka tattauna tare da ita tana da shekaru 38, kuma yanzu haka tana aiki ne a wani kamfanin da ke lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Kafin wannan kuma, aikin shara ne ta yi tare da mai gidanta a gairnsu, aikin da aka biya kowanensu yuan dubu daya a kowane wata, wanda bai ishe su wajen rayuwa ta yau da kullum ba. Don haka, a shekarar 2015, sun je lardin Guangdong.

Gaskiyar “aikin tilas”_fororder_微信图片_20210418214102

Dr.Nilufer Gheyret da kuma Dr.Chen Ning su ne marubutan wannan rahoto, wadanda kuma suka fito daga jihar Xinjiang, kuma Dr.Nilufer Gheyret ‘yar kabilar Uygur ce, a yayin da Dr.Chen Ning ta yi karatu na digiri na farko da na biyu ta fannin harshen Uygur.  Marubutan biyu sun ziyarci wasu kamfanoni biyar da ke lardin Guangdong, wadanda ke daukar ma’aikata ‘yan wasu kabilu da suka fito daga jihar Xinjiang, inda suka tattauna tare da ma’aikata kimanin 70 na kabilun Uygur da Kazak da Kirghiz da Tajik da sauransu, don fahimtar dalilan da suka sa su fita cin rani da kuma rayuwarsu ta yau da kullum.

Bisa ga binciken da suka gudanar, sun fahimci cewa, wadannan ma’aikata sun fita cin rani ne bisa son ransu, kuma kaso 36% daga cikinsu sun ce sabo da albashi mai tsoka da suke iya samu ne ya sa sun fita daga garinsu, a yayin da kaso 15% daga cikinsu sun ce irin kyakkyawan muhalli na rayuwa ne ya janyo su, kuma babu abin da ake kira “aikin tilas” da suka gano. Baya ga haka, a yayin tattaunawarsu da ma’aikatan, sun kuma bayyana fushi da kuma damuwa dangane da yadda wasu kasashen yammaci suka bayyana aikin da suka yi a kamfanonin a matsayin “aikin tilas”. Kamar wata mai shekaru sama da 40 daga cikin ma’aikatan ta ce, “Muna aiki ne bisa karfinmu, gwamnati ta ba mu wannan dama, amma wasu kasashen yammaci sun bayyana mu a matsayin masu aikin tilas, matakin da zai lalata damarmu ta aiki.”

Gaskiyar “aikin tilas”_fororder_微信图片_20210418214108

Burin kowa ne rayuwarsa ta dada inganta, kuma hakkin kowa ne ya inganta rayuwarsa bisa kokarin aiki. Akwai rashin daidaito na ci gaban tattalin arziki tsakanin sassan gabashi da yammacin kasar Sin, don haka, abu ya dace al’ummar wasu sassa na rashin ci gaba da ke yammacin kasar su fita cin rani a sassa masu ci gaba na gabashin kasar, don samun karin kudin shiga da kuma inganta rayuwarsu, amma me ya sa wasu ‘yan kasashen yammaci suke daukar lamarin a matsayin “aiki na tilas”?

A hakika, wasu kasashen yammaci masu kin jinin kasar Sin sun dade suna fakewa da sunan “kare hakkin bil Adam”, inda suka yi kokarin ta da rikici, don cimma burinsu na siyasa. Domin neman shafa wa kasar Sin bakin fenti, kwanan baya, har sun hada batun kiyaye muhalli da hakkin bil Adam. Kwanan baya, kafar BBC ta tattauna tare da shahararren masanin ilmin tattalin arzikin kasar Amurka Jeffrey Sachs dangane da batun sauyin yanayi. Sai dai abin mamaki shi ne yadda mai gabatar da shiri na BBC din ya fara da tambaya game da hakkin bil Adam na kasar Sin, lamarin da ya sa Mr.Sachs ya kasa hakuri, har ma ya ce, “me ya sa ba mu tattauna abubuwan da Amurka ta yi na keta hakkin bil Adam?”, kafin daga bisani ya fara jera matakan da Amurka din ta dauka na keta hakkin bil Adam a gida da kuma waje. A yayin da mai gabatar da shirin ke neman dakatar da shi, sai ya ce, “A yi hakuri, bari in gama maganar. Ina ganin shirin na da mamaki, kuma ya bambanta da yadda na yi zato. Kullum Amurka ne neman nuna wa wasu kasashe yatsa, amma na san yaya manufofin diplomasiyya na kasar ya kasance, kuma na san yadda ake ji a wata kasar da ke nuna kabilanci, sabo da ina rayuwa ne a kasar Amurka.”

Gaskiyar “aikin tilas”_fororder_微信图片_20210418214609

Akwai wasu masu bibbiyarmu a shafinmu na Facebook da su kan bayyana damuwarsu dangane da yanayin da al’ummar Uygur ke ciki a jihar Xinjiang. Misali, game da wani rahotonmu dangane da jihar Xinjiang da muka saka a kwanan baya, malam Abdulsalam Muhammad ya ce, “ya kamata ku ce jihar da gwamnatin China ke kuntatawa musulmi”. Lalle kam muna iya fahimtar yadda kuke kulawa da yanayin da ‘yan uwa musulmi ke ciki, amma kuma muna da tambaya, daga ina ne kuka samu labarin cewa “kasar Sin na kuntatawa musulmi”? Kun gani da ido ne? ko kuma kun samu labari ne daga kafofin yada labarai na yammaci?

Gani ya kori ji. Maxime Vivas, dan jarida ne na kasar Faransa, wanda kuma marubuci ne na littafin nan mai taken “Kawo karshen labaran bogi game da Uygur”, ya taba zuwa jihar Xinjiang har sau biyu, inda ya gane ma idonsa ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma na jihar. Ya taba bayyana cewa, kasashen yammaci su kan yi amfani da hotuna da kuma hoton bidiyo wajen zargin kasar Sin kan batun Xinjiang, sai dai akasarin wadannan “shaidu” ba su da bayanai game da lokaci da kuma wuri na daukarsu, “sabo da in an samar da bayanan, lalle za a karyata su.”

Jita-jita su kan tsaya ga masu idon basira, kuma kofar Xinjiang a bude take. Muna fatan aminanmu masu damuwa da Xinjiang ku samu damar zuwa wurin ku gani da idanunku yadda jihar ta kasance. Muna kuma fatan da kuke karanta rahotanni game da Xinjiang, za ku kara tunani don bambanta gaskiya da karya. Daidai kamar yadda Maxime Vivas ya ce, “Karya game da Xinjiang banza ne a gaban gaskiya, kuma lokaci zai shaida mana cewa, zargin da kasashen yamma suka yi wa Xinjiang kuskure ne.” (Lubabatu)