logo

HAUSA

WHO ta yi alkawarin taimakawa bunkasa amincin riga kafin COVID-19 a Afrika

2021-04-16 11:14:40 CRI

WHO ta yi alkawarin taimakawa bunkasa amincin riga kafin COVID-19 a Afrika_fororder_u=1888158005,3896614979&fm=26&gp=0

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce ta hada hannu da gwamnatocin Afrika da nufin bunkasa amincin riga kafin COVID-19 yayin da ake kara kaimi wajen bayar da allurar a nahiyar.

Daraktar hukumar a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti ta ce an bayar da muhimmanci ga kafa ingantattun tsarin sa ido domin tabbatar da cewa ba a samu mummunan tasirin riga kafi a tsakanin rukunonin mutanen da suka fi fuskantar barazana ba.

Cikin wata sanarwar da aka fitar a Nairobi, jami’ar ta ce kowanne allura da aka yi, na kara matsawa kusa da kawo karshen annobar. Aikin riga kafin muhimmin kokari ne, sai dai ba za a tabbatar da babu barazana ba. Tana mai cewa, kasashen Afrika sun dauki ingantattun matakan bibiya da sa ido kan wata alama ta barazana ko tasiri bayan karbar riga kafin.   

Har ila yau, ta ce dandalin sa ido kan aikin yin allurar riga kafi a Afrika dake karkashin WHO na marawa kasashen Afrika baya wajen karfafa sa ido domin tabbatar da cewa allurar ba ta yi wata barazana ba. A cewarta, ta ce masu sa ido daga Habasha da Afrika ta Kudu da Tanzania sun shiga aikin WHO na nazarin inganci da amincin riga kafin COVID-19 da aka amince su shiga cikin wadanda za a yi amfani da su a matakin gaggawa. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha