logo

HAUSA

Kazanci: titi mai tarihin shekaru dari a Xinjiang

2021-04-16 11:20:50 CRI

Kazanci: titi mai tarihin shekaru dari a Xinjiang_fororder_1

Kazanci, wani titi ne mai dogon tarihi na sama da shekaru 100 a gundumar Yarkant dake jihar Xinjiang ta kasar Sin, wanda aka gina a shekara ta 1870. A yaren Uygur, Kazanci na nufin mai sana’ar kera tukunya. Titin Kazanci ya samo sunan ne saboda a nan ne aka fi samun masu fasahar kerawa gami da sayar da tunkuyar karfe da ta tagulla.

Kazanci: titi mai tarihin shekaru dari a Xinjiang_fororder_2

Kazanci: titi mai tarihin shekaru dari a Xinjiang_fororder_3

A titin Kazanci, ban da masu sayar da tukwane, akwai shaguna da dama dake sayar da kayan al’adu da abinci da kuma amfanin gona, tare kuma da sauran wasu wuraren more rayuwa.

Kazanci: titi mai tarihin shekaru dari a Xinjiang_fororder_4

Kazanci: titi mai tarihin shekaru dari a Xinjiang_fororder_5

A watan Satumbar shekara ta 2019, gwamnatin gundumar Yarkant ta himmatu wajen raya harkokin yawon bude ido,  inda ta gyara titin Kazanci ya zama mai tsawon mita 1500, wanda ke kunshe da shaguna 363, tare da samar da guraben aiki ga mutane 960 a wajen. A shekarar kuma, adadin masu yawon bude ido da suka je tsohon garin gundumar ya kai miliyan 2.33, kana yawan kudin shigar da aka samu daga sana’ar yawon shakatawa ya kai kudin Sin Yuan miliyan 278.(Murtala Zhang)