logo

HAUSA

Yaushe Amurka za ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe?

2021-04-16 11:01:50 CRI

Yaushe Amurka za ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe?_fororder_1

Amurka ta ce, ta farfado da shawarwari da kasar Iran jiya Alhamis a birnin Vienna na kasar Austria, a wani kokari na ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran wadda aka daddale a shekara ta 2015. Tuni, jagoran addinin Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana cewa, in Amurka tana son dawowa yarjejeniyar, kamata ya yi ta soke tukunkumin da ta sanyawa kasarsa.

Bayan yakin duniya na biyu ya zuwa yanzu, Amurka ta dade tana tafiyar da manufar shiga sharo ba shanu cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, ciki har da kai harin soja, da sanya takunkumi, da tunzura masu tada rikici. Wato Amurka tana yin duk wani abun da za ta iya don nuna babakere a duk fadin duniya baki daya.

Bayan da Joe Biden ya hau karagar mulkin Amurka, ya sha nanata cewa zai maida hankali sosai kan batun hakkin dan Adam a cikin harkokin diflomasiyyar kasar. Wato Amurka tana fakewa da batun hakkin dan Adam don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, al’amarin da ya haddasa rikicin zubar da jini a sassa da dama a duniya. Tambayar a nan ita ce, idan wata kasa ta rasa ikon mulkin kai, ta yaya za ta kare hakkin dan Adam a kasar?

Yaushe Amurka za ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe?_fororder_2

A cikin sanarwar da aka fitar a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a shekara ta 1965, an ce, bai kamata wata kasa ta tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe ba duk hujjar da take da ita. Kada wata kasa ta yiwa sauran kasashe barazana ta hanyar daukar matakan siyasa da soja da kuma tattalin arziki don sauran kasashe su mika wuya. Bugu da kari, sanarwar ta ce, bai kamata wata kasa ta hura wutar rikici da tallafawa ayyukan kifar da gwamnatin sauran kasashe ba. Amma, ita Amurka, ta yi duka.

Duk da cewa annobar COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a duniya, Amurka ba ta dakatar da ayyukan ta na sanyawa sauran kasashe takunkumi ba, abun da ya illata hadin-gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar, da tsananta matsalar jin-kai a duniya.

Rashin yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, babbar manufa ce a cikin kundin tsarin mulkin MDD, wadda ta samu amincewa daga kasa da kasa. Yaushe Amurka za ta daina tsoma bakinta cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe?(Murtala Zhang)