logo

HAUSA

Ana sa ran tattalin arzikin Sin zai ci gaba da farfadowa

2021-04-16 21:47:33 CRI

Ana sa ran tattalin arzikin Sin zai ci gaba da farfadowa_fororder_1

Alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta sanar a yau Jumm’a, sun nuna cewa, a cikin rubu’in farko na bana, kuma gaba daya adadin GDPn kasar ya kai kudin Sin yuan biliyan 24931, adadin da ya karu da kaso 18.3 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Ko shakka babu, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a farkon shekarar bana, duk da cewa, kasar Sin ta gamu da matsala a watanni uku na farkon bara, amma yanzu haka tattalin arzikin kasar yana ci gaba da samun bunkasuwa kamar yadda ake fata, har saurin ci gabansa ya kai sahun gaba a fadin duniya.

Nan gaba kuma, kasar Sin za ta kasance kasuwar sayar da kayayyakin yau da kullum mafi girma a duniya. A sa’i daya, bukatunsa a fannonin shigowar kayayyaki da zuba jari tsakanin kasa da kasa, za su taimakawa farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya.

Har kullum tattalin arzikin kasar Sin, yana jawowa hankalin manyan kamfanonin ketare, saboda gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan kirkire-kirkire matuka.

Kana a cikin sabon rahoton hasashen tattalin arzikin da asusun lamunin duniya wato IMF ya gabatar, asusun ya riga ya daga hasashen karuwar tattalin arzikin kasar Sin na bana, daga kason 8.1 cikin dari zuwa 8.4 cikin dari. (Jamila)