logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Amurka zai taimakawa yakin da ake yi da sauyin yanayi

2021-04-15 16:58:34 CRI

Hadin gwiwar Sin da Amurka zai taimakawa yakin da ake yi da sauyin yanayi_fororder_微信图片_20210415163410

Duk da cewa yanayin alakar kasashen Sin da Amurka na fuskantar kalubale, da sabani a wasu muhimman sassa, a hannu guda, masharhanta na ganin hadin gwiwar kasashen biyu, zai taimaka wajen yakar matsalar sauyin yanayi, wanda tasirin yake haifar da bazarana ga rayuwar daukacin bil Adama.

Ana dai ganin sabuwar gwamnatin Amurka mai ci, na da sassaucin ra’ayi a fannin manufofinta na kare yanayi, inda tuni gwamnatin shugaba Joe Biden ta fara shiga shawarwari da sassan masu ruwa da tsaki, don gane da matakan yaki da sauyin yanayi, da kudurori masu alaka da burin cimma wannan nasara.

Da yake tun tuni, kasar Sin na da burin gina al’ummar gurguzu ta zamani mai wadata, da karfi da kyawawan akidun zamantakewar rayuwa, tare da fatan samar da al’ummar bil Adama mai makomar bai daya, hakan ya sa ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa, da sauke nauyin dake wuyanta, game da kare muhallin halittu, da dakile matsaloli masu nasaba da sauyin yanayi.

Idan an bi tarihi, za a ga yadda Sin ke cika alkawarin da ya dauka, na rage fitar da hayaki da sinadarai masu gurbata muhalli, wanda ya zarce irin matakan da kasashe manya da dama ke aiwatarwa. Tana kuma ci gaba da inganta da fadada gandayen daji, da aiwatar da manufofin kiyaye ruwa, da iska da sauran halittu abokan rayuwar bil Adama.

Ana sa ran cewa, hadin gwiwar Sin da Amurka a fannin kare muhalli, zai agazawa tsarin gudanarwa, na dakile tasirin sauyin yanayi. Alkaluma na nuna cewa, Sin da Amurka, a matsayin su na kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, kuma wadanda bisa jimilla suke fitar da kaso sama da 40 bisa dari na yawan hayakin dake tasiri ga muhalli, matakan da suke dauka a yanzu, za su yi babban tasiri ga yakin da duniya za ta yi da matsalar sauyin yanayi.

Karkashin wannan buri, masharhanta da dama, na ganin kafin cimma nasara, ya dace Sin da Amurka su kara fadada tattaunawa kan batun sauyin yanayi a matakai daban daban. Kazalika akwai bukatar su ci gaba da musayar bayanai game da hakan, ta yadda za su jawo ra’ayin karin kasashe su shiga wannan aiki mai matukar muhimmanci.

Ko shakka babu, idan Sin da Amurka suka tashi tsaye cikin hadin gwiwa, hakan zai zaburar da sassa irin su tarayyar Turai, da sauran nahiyoyi, wajen ba da tasu gudummawar kare muhalli, da dakile tasirin sauyin yanayi. Ta haka ne kuma duniya baki daya, za ta ci gajiya daga wannan muhimmin aiki na kare rayuwar bil Adama, zuriya bayana zuriya. (Saminu Hassan)