logo

HAUSA

Har yanzu ba a kawo karshen mulkin mallakar kasashen yamma ba

2021-04-14 22:51:13 CRI

Har yanzu ba a kawo karshen mulkin mallakar kasashen yamma ba_fororder_1

A kwanakin baya ne daraktar hukumar kiwon lafiyar duniya reshen nahiyar Afirka Matshidiso Moeti, ta fitar da wata sanarwa, inda ta nuna damuwa kan matsalar rashin adalci wajen rarraba allurar rigakarin cutar COVID-19, sakamakon alkaluman da aka samar, dake nuna yawan alluran rigakafin da aka yi wa al’ummomin kasashen Afirka bai wuce kaso 2 cikin dari kacal, cikin jimillar alluran da aka yi a fadin duniya ba.

Hakika mutane masu fahimtar tarihin mulkin mallakar kasashen yamma, ba su yi mamaki ba ko kadan kan hakan, saboda rarraba allurar rigakafin ba bisa adalci ba ya nuna cewa, rashin daidaito tsakanin kasa da kasa sakamakon kwace da ‘yan mulkin mallakar kasashen yamma suka yi a cikin shekaru sama da daruruwa da suka gabata har yanzu yana ci gaba da wakana.

An lura cewa, kasashe masu ci gaba, sun samu ci gaba ne ta wannan hanya, wato ta kwace dukiyoyi daga sauran kasashe, kana lamarin ya jefa wasu kasashe cikin mawuyacin yanayi har ya zuwa yanzu. Ban da haka, ana aiwatar da manufar nuna wariyar launin fata, da mayar da fararen fata gaban saura, sakamakon mulkin mallakar.

Haka zalika, tunanin mulkin mallaka yana gurgunta duniyarnu baki daya, inda wasu kasashen yamma suke kokarin ci gaba da yin tasiri ga kasashen da suka taba gudanar da mulkin mallaka, har suna tayar da hargitsi a kasashen.

Ko shakka babu, kasashen yamma sun samu ci gaba ne ta hanyar kwace dukiyoyin sauran kasashe, amma ba zai yiwu su cimma kudurin su na cin zalin sauran kasashe ba a halin da ake ciki yanzu, saboda an riga an kafa huldar demokuradiyya tsakanin kasa da kasa.(Jamila)