logo

HAUSA

An fara yiwa baki ’yan kasashen waje riga kafin COVID-19 a kasar Sin

2021-04-14 09:53:20 CRI

Bayanai na nuna cewa, ya zuwa yanzu an yiwa jimillar mutane sama da miliyan 165 rigakafin cutar COVID-19 a wurare daban daban na kasar Sin, wannan adadin shi ne na biyu na yawan rigakafin da aka gudanar a duk duniya.

An fara yiwa baki ’yan kasashen waje riga kafin COVID-19 a kasar Sin_fororder_210414-世界21013-hoto2

Baya ga rigakafin da ake yiwa jama’a cikin har da baki ’yan kasashen waje wadanda suka hada da ma’aikata da ’yan makaranta da sauransu, kasar Sin tana ci gaba da ba da gudummawar alluran rigakafi ga kasashe, musamman kasashe masu tasowa, lamarin dake tabbatar da alkawarin kasar na ganin riga kafin ta kasance hajar da duniya za ta ci gajiya.

Kasar Sin tana kuma karfafawa mutane gwiwar karbar alluran riga kafin COVID-19 bisa radin kansu, kuma tana kokarin tabbatar da dukkan mutanen da suka cancanci karbar riga kafin sun samu.

Jami’in hukumar kula da lafiya ta kasar Sin, Wu Liangyou, ya ce mutanen da suka zarce shekaru 18 na haihuwa, wato wadanda aka fi damawa da su cikin harkokin al’umma ne galibin wadanda suka karbi riga kafin.

An fara yiwa baki ’yan kasashen waje riga kafin COVID-19 a kasar Sin_fororder_210414-世界21013-hoto1

Ya kara da cewa, ba su kadai riga kafin zai ba kariya ba, har da iyalansu, musamman yara da tsoffi.

Kasar Sin tana gaggauta bada rigakafi tsakanin rukunonin mutane masu muhimmanci, tare da muhimman yankuna da birane. Masana sun jaddada cewa, har yanzu wannan annobar tana addabar wasu sassa na duniya, kuma har yanzu ba a kawar da yiwuwar barazanar shigo da cutar daga kasashen ketare ba.

Wannan riga kafi dai da ake yiwa baki ’yan kasashen waje, kyau ne. (Fa’iza, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)