logo

HAUSA

Cinikayyar wajen Sin ta samu babban ci gaba a farkon bana

2021-04-13 21:05:15 CRI

Cinikayyar wajen Sin ta samu babban ci gaba a farkon bana_fororder_1

Yau Talata, alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta samar sun nuna cewa, a rubu’in farko na bana, adadin kayayyakin da aka shigo da su kasar daga ketare, da kayayyakin da aka fitar zuwa ketare sun karu da kaso 29.2 cikin dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci a bara. A bayyane take cewa, cinikayyar wajen kasar Sin tana ci gaba da samun bunkasuwa, tun daga rubu’i na hudu na bara.

A halin da ake ciki yanzu, dalilin ci gaban cinikayyar waje cikin sauri a kasar Sin shi ne, tattalin arzikin duniya ya fara farfadowa, tun bayan da aka fara yin allurar rigakafin cutar COVID-19 a sassan duniya. A kasar Sin kuwa, ko a fannin masana’antu, ko a fannin zuba jari, ko kuma a fannin sayayya, dukkaninsu suna sa kaimi ga farfadowar tattalin arziki a kasar. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne, nasarar hana yaduwar cutar, da ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin, duka sun taka rawar gani ga gudanar da cinikayyar waje.

Kaza lika an lura cewa, kasar Sin tana kara bude kofa ga waje, domin samun karin ci gaban cinikayyar waje. Hakika ba ma kawai bude kofa ga waje na amfanar kasar Sin ba ne, har ma yana amfanar dukkanin duniya, saboda gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, zai samar da damammaki ga dukkanin duniya. (Jamila)