logo

HAUSA

Manufar wariyar launin fata ta Amurka na keta hakkin dan Adam

2021-04-13 20:03:25 CRI

Manufar wariyar launin fata ta Amurka na keta hakkin dan Adam_fororder_11

A shekarar 1962, marubucin kasar Amurka, ‘dan asalin Afirka James Baldwin, ya taba rubuta cewa, “Ina kai kara ga kasata da al’ummun kasata, bisa laifin nuna wariyar launin fata. Ko ni kaina, ko lokaci, ko tarihi, ba za mu yafe su ba, saboda sun aikata wannan laifin.”

Amma abun bakin ciki shi ne, kawo yanzu wato bayan shekaru kusan 60 da suka gabata, karar laifin da James Baldwin ya kai, tana ci gaba da wakana a kasar ta Amurka.

Alal misali, ana nunawa Amurkawa ‘yan asalin Asiya wariyar launin fata a yanzu. Rahoton da jami’ar jihar California ta Amurka ta fitar kwanan baya ya nuna cewa, adadin laifuffukan da aka aikata kan Amurkawa ‘yan asalin Asiya ya karu, da kaso har 149 cikin dari a shekarar 2020 da ta gabata.

An kuma lura cewa, dalilin hakan yana da nasaba da tsokacin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi inda ya ambaci “kwayar cutar kasar Sin” ko “murar Kongfu”, haka kuma yana da nasaba da manufar nuna wariyar launin fata ga ‘yan asalin Asiya.

Manufar wariyar launin fata ta Amurka na keta hakkin dan Adam_fororder_22

Hakika daukacin tsirarun al’ummun kasar Amurka, suna shan wahalar matuka. A halin yanzu, tsirarun al’ummun kasar sun samu allurar rigakafin cutar COVID-19 kalilan ne kawai, kuma alkaluman da asusun iyalin Kaiser ya samar, bayan da ya yi bincike a jihohi 41 dake kasar sun nuna cewa, ya zuwa ranar 6 ga wata, Amurkawa fararen fata dake jihohin 41, wadanda suka karbi allurar sau daya sun kai kaso 28 cikin dari, amma Amurkawa ‘yan asalin Latin Amurka da aka yi musu allurar ba su wuce kaso 16 cikin dari kacal ba, sai kuma ‘yan asalin Afirka da ke da kaso 17 cikin dari kacal.

A bayyane take cewa, ana aiwatar da manufar nuna wariyar launin fata daga duk fannoni a fadin kasar Amurka, lamarin da ya tono ainihin yanayi, da salon da demokuradiyyar Amurkake ciki. (Jamila)