logo

HAUSA

Ya Kamata Nahiyar Afrika Ta Dauki Darasi Daga Annobar COVID-19

2021-04-13 20:32:42 CRI

Ya Kamata Nahiyar Afrika Ta Dauki Darasi Daga Annobar COVID-19_fororder_微信图片_20210413170815

Har yanzu duniya na ci gaba da daukar matakan dakile cutar COVID-19 da ta addabe ta, inda a yanzu hankali ya karkata zuwa ga samarwa da rabawa da jigila da kuma uwa uba, bayar da riga kafin ga daukacin al’umma. A wannan gaba kuma, kasashe masu tasowa sun dukufa neman riga kafin, inda masu arziki suka saye mafi yawan riga kafin, ko kuma su da kansu suke samar da shi.

Yayin wani taron da aka yi jiya, kan samar da riga kafi a nahiyar Afrika, Darakta Janar ta kungiyar kula da cinikayya ta duniya WTO, ta ce ya zama wajibi nahiyar Afrika ta dauki matakan tabbatar da samar da nata alluran riga kafin, domin annobar da ake fama da ita a yanzu da wadanda ka iya zuwa a nan gaba.

Yadda annobar ta barke ba tare da wani gargadi, ya isa zama darasi ga kasashen don su tashi su kare kansu da daukan matakan kandagarki. Har ila yau, ya nuna cewa muddun dan Adam na raye, to dole ne ya shiryawa fuskantar annoba tun da ba ta sanar da zuwanta, sai dai a ganta kwatsam.

Nahiyar Afrika na da kwararru da tarin albarkatu ga kuma yawan jama’a, wadanda abubuwa ne da ake bukata domin ingiza ayyukan samun ci gaba. Sai dai, idan har ba a samu kwarin gwiwa daga gwamnatoci da shugabanni ba, to haka za a yi ta zama kan wadannan albarkatu ba tare da an ci gajiyarsu ba.

Misali, kasar Sin a matsayinta na kasa mai yawan al’umma a duniya, ta jajirce bisa shugabanci na gari da daukar dabarun da turbar da suka dace ta, wajen raya kanta. Jimilar al’ummar kasar sama da biliyan 1.4, sun zarce jimilar al’ummar Afrika baki dayanta dake da biliyan 1.3 da doriya. Amma abun mamaki shi ne, wannan kasa dake da tarin nauyi a wuyanta ce ke samar da tallafin riga kafi ga kasashen Afrika, baya ga dogaro da ita da suka yi a fannoni da dama. Zuwa yanzu, kasar Sin ta samar da riga kafin COVID-19 ga kasashen nahiyar sama da 30, wanda dori ne kan taimakon da ta rika ba su tun bayan bullar cutar, duk da cewa ita ma a lokacin, tana fama da ita.

Alkaluman WHO sun nuna cewa, kasa da kaso 2 na wadanda aka yi wa riga kafin cutar ne kadai Afrika ta dauka, duk kuwa da yawan al’ummarta. Idan a ce nahiyar na da karfin samar da riga kafin da kuma kayayyakin yaki da annobar, mai yuwuwa da zuwa yanzu, ta shawo kanta kamar yadda Sin ta yi. Yunkurin nahiyar wajen sauya kanta, zai yi gagarumin tasiri wajen rage nauyin da take dorawa wasu kasashe tare da bada gudunmawa mai yawa ga ci gaban duniya da wanzuwar zaman lafiya da wadata. Ya kamata kasashen nahiyar su kara sauya salonsu, su dauki darasi daga kasashen da suka ci gaba kamar Sin, domin su ma a nan gaba su kare kansu tare da bada gudunmawa, maimakon zama nauyi.  (Fa’iza Mustapha)