logo

HAUSA

Saifullahi Aminu Bello: Ina alfahari da jami’ar Xiamen mai tarihin shekaru 100!

2021-04-13 14:24:31 CRI

Saifullahi Aminu Bello: Ina alfahari da jami’ar Xiamen mai tarihin shekaru 100!_fororder_1

Kwanan nan ne, jami’ar Xiamen a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin ta yi bikin cika shekaru dari da kafuwa, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ma ya aike da sakon taya ta murna.

Saifullahi Aminu Bello: Ina alfahari da jami’ar Xiamen mai tarihin shekaru 100!_fororder_2

A sakonsa, shugaba Xi ya ce, jami’ar Xiamen, jami’a ce mai nagartacciyar al’ada. Tun kafuwar ta zuwa yanzu, bisa jagorancin akidun Tan Kah Kee, wato shahararren mai kishin kasa wanda ya kafa makarantar, jami’ar Xiamen ta himmatu wajen samar da ilimi ga mutane masu tarin yawa, wadda ta bayar da babbar gudummawa wajen gina kasa, da kyautata rayuwar al’umma gami da tallata al’adun kasar Sin zuwa kasashen ketare.

Har wa yau, bana ake cika shekaru 100 da kafa jam’iyya mai mulki a kasar Sin, wato jam’iyyar kwaminis ta kasar. Wato, bana, jam’iyyar kwaminis da jami’ar Xiamen suke bikin murnar cika shekaru 100 da kafuwa.

Saifullahi Aminu Bello: Ina alfahari da jami’ar Xiamen mai tarihin shekaru 100!_fororder_微信图片_20210413133843

A daidai wannan lokaci, Murtala Zhang ya zanta da daya daga cikin daliban Najeriya da suke karatu a jami’ar Xiamen, malam Saifullahi Aminu Bello, dan jihar Kano wanda ke karatun digiri na uku a fannin na'ura mai kwakwalwa a jami’ar. Ya bayyana farin cikin sa sosai ga cikar jami’arsa shekaru 100 da kafuwa, ya kuma yi tsokaci a kan muhimmiyar rawar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ke takawa a fannin raya harkokin kasar.

Malam Saifullahi Aminu Bello ya kara da cewa, kishin kasa da sadaukarwar da ‘yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin suke yi, ya burge shi kwarai da gaske.(Murtala Zhang)