logo

HAUSA

Salon demokuradiyyar Amurka na gurgunta zaman lafiyar duniya

2021-04-12 21:23:07 CRI

Salon demokuradiyyar Amurka na gurgunta zaman lafiyar duniya_fororder_11

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, yanayin siyasar Ukraine yana kara tsanani, sakamakon tsoma bakin kasar Amurka, inda bangaren sojojin Amurka ya sanar da cewa, zai tura jiragen ruwan yakinsa zuwa yankin Black Sea, kuma shugaban kasar da sakataren harkokin wajen kasar, da sauran manyan jami’an kasar ta Amurka, suna gudanar da shawarwari da hukumomin da abin ya shafa na kasar Ukraine.

Kwanan baya, cibiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto, inda aka bayyana cewa, tun daga yakin duniya na biyu, kusan daukacin shugabannin kasar Amurka sun taba bayar da umurnin yin yake-yake, kuma domin boye ainihin laifinsu na kai hari, Amurka ta saba da karaikayi iri daban daban. Alal misali, “hakkin dan Adam ya fi ikon mulkin kasa muhimmanci”, ko “daukar matakin jin kai”, amma ba zai yiwu ta cimma burinta ba.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, Amurka tana kokarin daukar matakan gurgunta daukacin kasashen da ba su so su bi umurninta, domin kiyaye hakkinta na nuna fin karfi.

Hakika, matakan da Amurka ta dauka su ma suna kawo matsala ga ita kanta, tare da bata kimar kasar a fadin duniya.

A don haka, ya dace ‘yan siyasar Amurka su maimaita kashedin da Henry Alfred Kissinger ya rubuta, a cikin littafinsa na “Tsare-tsaren Amurka a fadin duniya”, inda ya bayyana cewa, matakin nuna fin karfi zai rushe burin Amurka na kasancewa babbar kasa a duniya. (Jamila)