logo

HAUSA

Riga-kafin COVID-19 a kasar Sin: Ni ma shaida ne

2021-04-12 15:40:00 CRI

 

Riga-kafin COVID-19 a kasar Sin: Ni ma shaida ne_fororder_微信图片_20210412145610

Ko shakka babu masu azancin magana na cewa, “gani ya kori ji.”

Yayin da kasar Sin ta himmatu wajen daura aniyar gudanar da riga-kafin annobar COVID-19 ga kafatanin al’ummar kasar, a halin yanzu za mu iya cewa tafiya ta yi nisa matuka game da aikin riga-kafin shu’umar cutar sarkewar numfashi ta COVID-19 a dukkan sassan kasar Sin. Sai dai wani abin ban sha’awa shi ne, yadda har kullum kasar Sin ba ta “yin tuya ta mantawa da albasa.” Abin nufi shi ne, duk da irin yadda kasar ta sha alwashin yiwa jama’arta riga-kafin annobar, a hannu guda kuma, ba ta mantawa da takwarorinta wato baki ’yan kasashen waje dake aiki, ko kuma dalibai dake karatu a kasar ta Sin ba. A makonnin baya bayan nan, kasar Sin ta bada sanarwar yiwa baki ’yan kasashen waje mazauna kasar riga-kafin annobar COVID-19 a kyauta ba tare da biyan koda sisin kwabo ba, sannan ga wadanda ke da sha’awa ba tare da yin tilas ba. Wannan ya bada dama ga baki ’yan kasashen na samun riga-kafin cutar ta COVID-19, cikin mutanen da suka samu riga-kafin har da ma’aikatan babban rukunin gidan radiyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG, wanda ya gudana a karshen mako. Hakika, ni kaina shaida ne, domin na karbi wannan allurar riga-kafin cutar COVID-19 ta kamfanin Sinovac Biotech, kuma ba tare da fuskantar wata matsala ba, har ma na shafe wasu kwanaki da dama bayan karbar riga-kafin ba tare da samun wata matsalar rashin lafiya ko kuma sauyawar yanayin lafiyar jiki ba. Ko shakka babu, wannan allurar riga-kafin na da inganci sosai. Don haka ni ma shaida ne. Kawo yanzu, za mu iya cewa, tafiya ta yi nisa game da aikin riga-kafin cutar COVID-19 a kasar Sin. Kamar yadda rahotanni daga taron manema labarai na hadin gwiwa tsakanin gamayyar kwamitin yaki da annoba na majalisar gudanarwar kasar Sin wanda aka gudanar a ranar 11 ga wannan wata na Afrilu ya nuna cewa, kasar ta kai matsayi na biyu a duniya na yawan adadin mutanen da aka yiwa allurar riga-kafin cutar COVID-19. Wu Liangyou, mataimakin daraktan hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar Sin CDC ta ma’aikatar lafiyar kasar ya bayyana a taron manema labarai cewa, a halin yanzu, ana gudanar da aikin allurar riga-kafin cutar COVID-19 a kasar yadda ya kamata. Ya zuwa ranar 10 ga watan Afrilu da muke ciki, an yiwa jimillar mutane miliyan 164.471 riga-kafin cutar COVID-19 a wurare daban daban na kasar, kuma adadin shi ne na biyu na yawan riga-kafin da aka gudanar a duk duniya.

Masana sun jaddada cewa, har yanzu wannan annobar tana matsayin koli a duniya, kuma har yanzu tana kan ganiyarta domin ba a kawar da yiwuwar barazanar shigo da cutar daga kasashen ketare ba. A hannu guda kuma, barazanar yaduwar annobar a cikin gida wanda ake fuskanta sanadiyyar shigowa da cutar daga ketare har yanzu yana ci gaba da wanzuwa, don haka, ba zai yiwu a sassauta matakan kandagarkin hana bazuwar annobar a halin yanzu ba. (Ahmad Fagam)