logo

HAUSA

Ra'ayin Kasar Amurka Dangane Da Yanayin Hakkin Dan Adam Na kasar Najeriya

2021-04-12 18:45:27 CRI

Ra'ayin Kasar Amurka Dangane Da Yanayin Hakkin Dan Adam Na kasar Najeriya_fororder_20210412-sharhi-Bello-2

A karshen watan da ya gabata, majalisar gudanarwar kasar Amurka ta sanar da rahoton da ta kan gabatar a kowace shekara dangane da yanayin hakkin dan Adam na kasashe daban daban na 45, inda a cikin rahoton an yi suka sosai kan yanayin hakkin dan Adam na kasar Najeriya. An ce, ana ganin abkuwar munanan ayyukan keta hakkin dan Adam da yawa a Najeriya, wadanda suka hada da tsare mutum ba bisa doka ba, da yin amfani da karfin tuwo fiye da kima kan ‘yan zanga-zanga, da kashe mutanen da ake zarginsu da laifi ba tare da bin matakan shari’a ba, da dai sauransu. Cikin wannan rahoton da kasar Amurka ta gabatar, an kwatanta sojoji da ‘yan sandan kasar Najeriya da ‘yan ta’addan kasar, inda aka ce dukkansu suna keta hakki na mutane (ta hanyar jefa su cikin kurkuku ba tare da wani dalili ba, ko kuma ta hanyar sace su), da azabtar da fararen hula, da kuma kashe su. Kana ana kokarin kare sojojin da ‘yan sandan da suka aikata laifin, da sanya su magance fuskantar hukunci. Haka zalika, a cikin rahoton, kasar Amurka ta nuna shakku kan hukumar shari’a ta kasar Najeriya, inda ta ce ba ta da wani matsayi na mai zaman kanta, kana ta kan kwaci wasu bayanan da jama’a ba su so su nunawa sauran mutane. Kamar yadda aka bayyana a cikin rahoton, kasar Najeriya wata kasa ce, da ta ki baiwa jama’arta isassun damammakin fadi ra’ayi, da kulla kungiyoyi, da kuma bin addini.

Ban san ainihin abun da yake cikin zukatanku ba, bayan da kuka gan rahoton. Sai dai na ji akwai tambayoyi guda 2: Na farko, me ya sa kasar Amurka ce ta rubuta wannan rahoto? Sa’an nan na biyu, shin wannan rahoto yana da gaskiya?

Game da tambayar ta farko, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya rubuta a cikin rahoton cewa: “Kasar Amuka tana dora matukar mihimmanci kan hakkin dan Adam yayin da take hulda da sauran kasashe”, don haka majalisar gudanarwar kasar na neman tattara bayanai game da hakkin dan Adam na kasashe daban daban, da samar da su ga mutanen kasashe daban daban, don sanya su “daukar matakan na hana abkuwar aikace-aikacen keta hakkin dan Adam”. Ta wannan magana, za mu iya ganin cewa, kasar Amurka tana kallon kanta a matsayin “mai kare hakkin dan Adam a duniya”. Sai dai wannan kasa dake kokarin “kare hakkin dan Adam a duk duniya, a hakika wane yanayin ake ciki ne a gidanta, a fannin hakkin bil Adama?

Dokta Martin Luther King ya sadaukar da ransa don kare hakkin bakaken fata dake kasar Amurka wasu shekaru 53 da suka wuce, amma har zuwa yanzu, ‘yan asalin Afirka dake zama a kasar na ci gaba da kokarin faftuka don kare hakkinsu na rayuwa. A watan Mayun bara, George Floyd, wani dan asalin Afirka mai shekaru 46 a duniya, ya mutu sakamakon yadda wasu ‘yan sanda masu farin fata suka kai masa hari ba gaira ba dalili, inda wani dan sanda ya gurfana a kan wuyansa har tsawon muntuna 8, lamarin da ya haddasa mutuwarsa nan take. Bidiyon da aka nuna a kan shafukan yanar gizo ta Internet, game da yadda dan sandan ya kashe Mista Floyd, ya fusata al’ummun kasar Amurka sosai, har ma ya sa aka kaddamar da babbar zanga-zangar nuna takaicin yadda ake cin zarafin bakaken fata a kasar Amurka ta “Black Lives Matter”. Sai dai mutanen da suka yi kama da George Floyd suna da yawa, amma babu wani bidiyon da zai nuna yadda aka ci zarafinsu. Ko da yake yawan ‘yan asalin Afirka ya kai kashi 13% na yawan al’ummar kasar Amurka kawai, amma bakaken fata sun kai kashi 1 bisa kashi 3 na daukacin ‘yan kason kasar, gami da kashi 28% na mutanen da ‘yan sandan kasar suka kashe. Wadannan alkaluma sun nuna yadda ake samun matsalar bambancin kabilu da na launin fata sosai a kasar Amurka. Kasar da ta kasa kare rayuka da hakki na tushe na jama’arta, tana iya zama “mai kare hakkin dan Adam a duniya” ? Ban sani ba me ya sa kasar take jin kamar tana da iko, don ta tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe?

Ban da wannan kuma, wani babban abin tambaya shi ne, wannan rahoton da kasar Amurka ta hada yana da gaskiya ne? Musamman ma ta la’akari da yadda aka wallafa shi, da bayanan da ya kunsa? A cikin rahoton, an rubuta cewa, gidajen jakadancin kasar Amurka dake kasashe daban daban su ne suka dauki nauyin wallafa babi game da kasashen da suke ciki, sa’an nan sun mika ma majalisar gudanarwar kasar Amurka don ta hada su waje guda. Wannan tsarin da aka bi wajen hada rahoton, ya sa bayanan dake ciki ke wakiltar ra’ayi na kasar Amurka kawai, musamman ma yadda kasar take kallon sauran kasashe. Abubuwa da yawa dake cikin rahoton ya saba wa gaskiya. Misali, a cikin babin da ya shafi yanayin hakkin dan Adam na kasar Sin, an yi kokarin dora wa gwamnatin kasar Sin laifin cewa “tana yin kisan kiyashi kan ‘yan kabilar Uygur”. Sai dai mene ne gaskiyar batun? Ana iya ganin hakikanin abun da ya faru ne ta hanyar nazari kan wasu alkaluman da aka samu ta hanyar kirgar al’umma: Daga shekarar 2010 zuwa ta 2018, yawan ‘yan kabilar Uygur ya karu daga miliyan 10.17115 zuwa miliyan 12.7184, adadin da ya karu da miliyan 2.5469, kimanin kashi 25.04%. Idan mun dubi tarihin dan Adam, za mu ga yadda ‘yan Nazi na kasar Jamus suka yi kisan kiyashi kan Yahudawa, lamarin da ya haddasa mutuwar Yahudawa kimanin miliyan 6, da raguwar yawan Yahudawa a nahiyar Turai da rabinsu. Sai dai wa ya taba ganin wani “kisan kiyashi” da ya sa yawan al’umma ke ta samun karuwa cikin sauri? Amurka tana zargin kasar Sin da yin kisan kiyashi ne bisa wani “rahoton nazari” da wani dan kasar Jamus mai suna Adrian Zenz ya gabatar. Sai dai wannan mutumin ya yi kaurin suna wajen yin karairayi, da gyara alkaluma, gami da matukar kin jinin kasar Sin. Ta wannan za a iya ganin yadda ake kokarin karkata ga wani bangare don bayyana ra’ayin kai a cikin wannan rahoton da kasar Amurka ta gabatar.

Hakika dai, kamar yadda wani karin magana ya bayyana, “Abokin kuka, shi ake gayawa mutuwa.” duk wata kasa, ko daidaikon mutane, suna bukatar samun shawarwari daga sauran mutane. Amma, dole ne a tabbatar da cewa, a ba da shawarwarin ne bisa niyya ta gari, da la’akari da hakikanin yanayin da ake ciki, maimakon bisa wata muguwar niyya ta shafawa wani kashin kaza, da kokarin yada jita-jita. Saboda haka, game da rahoton da kasar Amurka ta gabatar, kan yanayin hakkin dan Adam na kasar Najeriya, kafin mu amince da shi, ya kamata mu yi nazari a kansa cikin tsanake, don duba ko akwai gaskiya a ciki, kana ko an gabatar da rahoton ne bisa wata niyya ta gari. (Bello Wang)

Bello