Sauke nauyin da ke bisa wuyan “iyali mafi nagarta na kasar Sin” ta hanyar yada wakar Daben ta gargajiya
2021-04-12 20:07:32 CRI
Mawakin gargajiya Zhao Piding, fitacce ne a birnin Dali dake lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin. An shafe shekaru da dama Zhao na jajircewa wajen gado da inganta fasahar gargajiya ta wakar Daben ta kabilar Bai. Bisa kwarin gwiwar da suka samu daga Zhao, zuri’a 3 ta iyalansa, sun kafa wata tashar rediyo da wajen horar da wakar Daben da tawagar masu wake-wake, domin yayata wakar.
An haifi Zhao Piding dake tinkarar shekaru 80, a kauyen Zuoyi na garin Xizhou, dake birnin Dali. Danginsa, ciki har da kakannin kakanninsa, sun yi fice wajen rera wakar Daben a garinsu. Iyayensa da ‘yan uwansa maza ma sun kware wajen rera wakar da amfani da kayayyakin waka na gargajiya. Tun Zhao yana karami, ya yanke shawarar zama mawaki kamar iyayensa da yayunsa.
A yayin da yake da shekaru 15, Zhao ya taba rera waka a dandalin kauyensu, inda ya rera salon wakar Daben ta gargajiya ta Liang Zhu wanda ke nufin soyayyar malam bude littafi. Kokarin da ya yi, ya samu yabo sosai. A shekarar 1974, wani kauye dake garin Xizhou, ya gayyaci Zhao, domin rera wakar Daben kai tsaye gaban jama’a. Wannan wasa ya sa Zhao ya yi fice a Xizhou. A sakamakon haka, ya fara wasa akai-akai a matsayin fitaccen mawakin kabilar Bai daga Dali.
Ba sana’a kadai wakar Daben ta samarwa Zhao ba, har ma da soyayya. A lokacin da yake cikin shekaru 20, ya hadu da wata mata, ita ma ‘yar kabilar Bai, yayin wata wasa da ya yi a gari Xizhou. Zhao ya hadu da matar ne a lokacin da gajeren hutu na wasa. Ita ma tana wakar Daben. Su biyun, sun rera wakar tare. Zhao ya fara son matar, wato Zhao Lihui, wadda daga baya ta zama matarsa.
Sun yi aure a karshen shekarar 1966. Suna da ‘yan mata 4 da yaro 1. Zhao Piding na rayuwa ne kan wakar Daben.
Tun Zhao yana da shekaru 3 a duniya yake da matsalar a kafarsa ta hagu. Lamarin dake ba shi wahalar tafiya. A don haka, Zhao Lihui ce ke kula da iyalin. Musammam a lokacin da yaransu ke kanana, Zhao Lihui ce ke kula da yaran 5. Kuma ita ce ke kula da ayyukan gida. Zhao Lihui, wadda ita ma ke son wakar Daben, ta koyawa ‘yayanta rawa da rera wakar a lokacin da suke kanana.
Saboda tasirin iyayensu, 4 daga cikin yaran, sun zama mawakan gargajiya. Kuma kowannensu ya iya rera wakar Daben sosai. ‘Yarsu ta 2 wato Zhao Dongmei, ta fara rera waka ne tare da mahaifinta a lokacin da take shekaru 11. Zhao Fukun, wanda shi kadai ne namiji, ya bar aikin da yake yi a wajen garinsu, ya koma gida domin taimakawa mahaifinsa raya al’adar gargajiyar ta kabilar Bai.
Cikin shekaru 50 da suka gabata, ‘ya’yan Zhao Piding da jikokinsa, sun sake tsara fasalin wakar Daben zuwa raye-raye da wasannin kwaikwayo karkashin jagorancinsa, abun da ya inganta hanyar gabatar da al’adar ta gargajiya.
Zhao Piding ya yi fice a kauyen saboda kirkinsa. A lokacin da Shugaba Xi Jinping ya ziyarci lardin Yunnan a shekarar 2015, ya yi kira ga al’ummar Yunnan da su kare muhallin tafkin Erhai.
Domin karfafa gwiwar al’ummar kabilar Bai taimakawa kare tafkin Erhai, Zhao Piding da ‘ya’yansa sun hada wakoki da dama. Sun yi amfani da fasahar wakar Daben wajen wayar da kan al’umma kan kare muhalli. Dukkan ‘ya’yansa sun goya masa baya a kokarinsa na yin kyawawan ayyuka a kauyensu.
A lokutan da ba su da aiki, Zhao Piding da ‘ya’yansa kan gudanar da wasa kyauta, domin taimakawa mutanen kabilar Bai fahimtar matakai da dabarun kare muhalli ta hanyar sauraron wakoki.
A cewar Zhao Fukun, “babana ya sadaukar da kanshi wajen kare tafkin Erhai, kuma yana amfani da sabbin waken Daben, a matsayin dabarar yada muhimmancin kare tafkin”.
Iyalin Zhao sun kirkiro wani shirin wasan fasaha mai suna “Hua Shang Hua” wato “Fure a kan Fure”. Zhao Fukun na rubuta wasannin kwaikwayo. ‘Yan uwansa mata biyu kuma, suke fitowa a wasannin yayin da shi kuma yake kula da ayyukan bayan dandali. Daya uwar tasa kuma kan bada hidimar samar da cimaka.
Daga cikin ‘yan uwan 5, Zhao Fukun da ‘yar uwarsa ta biyu na da kantuna a Dali. Idan iyalinsu na wasa, su biyun kan rufe shagunansu su koma kauye don a yi tare da su. Wani ya taba yi wa Zhao Fukun tambaya cewa, kana da kanti kuma kasuwancinka na tafiya da kyau. Me ya sa wata rana kake rufewa don gudanar da wasa kyauta? Meye amfanin hakan? Zhao Fukun ya amsa da cewa: “zan iya samun kudi daga baya. Amma na yi imani da furucin mahaifina cewa, idan za mu iya kare tafkin Erhai da kyau, za mu iya jan hankalin karin masu ziyartar Dali, kuma a sannan, dukkanmu za mu fi kyautata kasuwancinmu cikin lokaci mai tsawo. Kare tafkin Erhai, na nufin kare kanmu da ‘ya’yanmu.”
A yanzu, Zhao Piding na yawan amfani da kujerar kuragu yayin da iyalinsa ke wasan rera wakar Daben. Ya kafa misali ga matasan garinsu, kuma ya taimakawa wasu raya fasahohin gargajiya da al’adu.
A baki dayan shekarar da ta gabata, a matsayinsu na wadanda aka karrama a matsayin “iyali mafi nagarta na kasa” sun shiga an dama da su a yakin da al’ummar Sinawa suka yi da cutar COVID-19. Zhao Piding ya ce,“na ga likitoci da dama da ma’aikatan jinya da ‘yan sanda da masu aikin sa kai, suna sadaukar da kansu wajen kula da lafiyar mutanenmu. Bayan na lura wasu mutanen kauyenmu ba su da wayewa da ilimin kandagarkin cutar, sai na yi tunanin dole in yi wani abu domin taimaka musu.”
Ya kalli shirye-shiryen talabijin da sauraron na rediyo, domin koyon dabaru da matakan kiwon lafiya da gwamnatin kasar Sin ta gabatar. Sai ya tattara bayanai masu muhimmanci, ya mayar da su wakoki da nufin wayar da kan jama’a kan matakan kandagarkin cuta da hanyoyin kare lafiya.
Da taimakon ‘ya’yansa, Zhao Piding ya tsara wakokin Daben 3 ga al’ummar Bai dake garinsu domin taimaka musu fahimtar dabaru da matakan kiwon lafiya. A lokacin da ake tsaka da yaki da annobar COVID-19, Iyalin Zhao, sun kara sabon kuzari wajen gado da raya wakar Daben ta ‘yan kabilar Bai.
Masu sauraro, yanzu kuma bari mu shakata kadan, daga baya kuma za mu shiga sashen “Akushin Sinawa”, inda Madam Fatimah Jibril za ta koya muku yadda za a dafa wani nau’in abincin Sinawa. Kafin mu je ga bude wannan Akushi, ‘yan uwana mata masu sauraronmu da ma masu sha’awar girke girken Sinawa, sai ku nemi takarda da alkalami domin ku samu damar rubuta abubuwan da zasu fada, domin kuwa a yau za ku koyi yadda ake dafa “cinyen kaji da aka yi cikin kori” ne.