logo

HAUSA

Sin Ta Samar Da Muhimmiyar Gudummawa Wajen Kiyaye Muhallin Halittu Na Duniya

2021-04-11 18:19:23 CRI

Sin Ta Samar Da Muhimmiyar Gudummawa Wajen Kiyaye Muhallin Halittu Na Duniya_fororder_IMG_6329.JPG

A sakamakon yaduwar cutar COVID-19 a duniya, an kara maida hankali ga dangantakar dake tsakanin dan Adam da muhallin halittu, kana an kara sa lura ga sauyin yanayi na duniya.

Yayin da ake tinkarar matsalolin duniya, Sin ta sanar da kara samar da gudummawa wajen kiyaye muhallin halittu na duniya. Shirye-shiryen Sin da ayyukan Sin sun kara sa kaimi ga kafa tsarin kiyaye muhallin halittu na duniya da kuma farfado da tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba.

Kiyaye muhallin halittu yana da nasaba da makomar dan Adam, raya zamantakewar al’umma ba tare da gurtaba muhalli ba shine burin bai daya na dukkan bil Adam. Don haka ana bukatar kasa da kasa su yi kokari tare don kiyaye muhallin halittu da tinkarar sauyin yanayi tare.

Sin ta kiyaye kokari don raya duniya mai tsafta, kamar kara sa kaimi ga cimma yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta Paris zuwa aiwatar da yarjejeniyar tsarin sauyin yanayi ta MDD a dukkan fannoni, da kuma kara sa kaimi ga raya shawarar “ziri daya da hanya daya” ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma batun shiga aikin kiyaye muhallin halittu na duniya.

Sin ta cimma burin rage fitar da iska mai gurbata yanayi na shekarar 2020 a karshen shekarar 2019.

Sin ta kafa tsarin samar da makamashi mai tsafta mafi girma a duniya, yawan na’urorin samar da wutar lantarki ta hanyoyin karfin ruwa, da karfin iska, da hasken rana a kasar Sin ya kai matsayi na farko a duniya.

Sin ta gina wuraren kiyaye muhallin halittu iri daban daban fiye da dubu 11.8, muraba’insu ya kai kashi 18 cikin dari bisa na dukkan yankunan kasar da kuma kashi 4.6 cikin dari bisa na dukkan tekun kasar, a cikinsu yawan wuraren yawon shakatawa na halittu na duniya da aka gina a kasar Sin ya kai matsayin farko a duniya.

Bayan shekarar 2000, muraba’in sabbin itatuwan da aka shuka a kasar Sin ya kai kashi daya cikin hudu bisa na duniya.

Hadin gwiwa zai sa kaimi ga samun ci gaba mai dorewa. Sin ta tsaya tsayin daka kan ra’ayin bangarori daban daban, kana tana son kiyaye muhallin halittu tare sauran bangarori na duniya, da shiga aikin kiyaye muhalli na duniya, da kuma yin kokari tare da kasa da kasa don samun bunkasuwa ba tare da gurtaba muhalli ba.

Ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta yi hadin gwiwa da mu’amala tare da kasashe fiye da 100 wajen kiyaye muhalli, da kuma daddale yarjejeniyoyin kiyaye muhallin halittu kimanin 150 tare da kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 60.

Za a samu ci gaba mai dorewa idan aka kiyaye muhalli mai kyau. Sin ta samar da muhimmiyar gudummawa wajen kiyaye muhallin halittu na duniya. Ya kamata kasa da kasa su yi kokari tare wajen tinkarar kalubalolin duniya tare. Hadin gwiwa ce kadai hanya mafi dacewa ga kasa da kasa a wannan fanni, ba za’a taba iya cimma burin ci gaban duniya bisa ra’ayin bangare daya ba. (Zainab)