logo

HAUSA

Ci gaban kasar Sin a fannin fasaha ba ya tsoron danniyar Amurka

2021-04-10 21:31:08 CRI

Ci gaban kasar Sin a fannin fasaha ba ya tsoron danniyar Amurka_fororder_0410-1

A ranar 8 ga wata, ma’aikatar kasuwanci ta Amurka ta sanar da cewa, za a sanya kamfanonin kasar Sin guda bakwai da ke da hannu a kera manyan kwamfutoci, cikin jerin sassan da kasar ke haramtawa a fannin kasuwanci. Wannan shi ne karo na farko da gwamnatin Biden ta fadada jerin sunayen sassan domin murkushe kamfanonin kasar Sin tun lokacin da ta hau karagar mulki, wannan kuma ya nuna a bayyane cewa, gwamnatin Amurka a yanzu na ci gaba da manufar tsohuwar gwamnatin ta matsa wa kamfanonin kasar Sin lamba, kana da karfafa murkushe kamfanonin kimiyya da fasaha na zamani na kasar ta Sin.

Dangane da wannan, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, tuni dai kasar Amurka ta soma daukar matakan killace kasar Sin a fannin manyan kwamfutoci, amma har yanzu manyan kwamfutocin na kasar Sin sun tsallake zuwa matsayin da ke kan gaba a duniya ta hanyar yin kirkire-kirkire. Kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace don kiyaye halaltattun hakkoki da muradun kamfanonin kasarta.

Domin kiyaye matsayinta na mallaka a duniya a fannin kimiyya da fasaha, da kuma dakile ci gaban kasar Sin, gwamnatin Amurka ta sha yin amfani da karfin kasa, da cin zarafin jerin sunayen sassan da ta haramta a fannin kasuwanci, don murkushe kamfanonin kimiyya da fasaha na zamani na kasar ta Sin ta kowace hanya. Ba sa kawar da yiwuwar bunkasa hadin gwiwa da kasar Sin wanda zai amfanawa Amurkar. A lokaci guda, ta jaddada yin hadin gwiwa da kawayenta don hana ci gaban kasar Sin, don murkushe kasar Sin a karshe.

Amma, kasar Sin ba ta jin tsoron irin wannan danniyar. A cikin shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta zarta Amurka, inda ta jagoranci duniya a kan yawan masu neman izinin mallakar fasaha. Daga shekarar 2010 zuwa 2019, yawan aikace-aikacen neman izinin mallakar wadannan fannoni ya kai kimanin 340,000, inda kasar Sin ta kai kashi 40%, kuma Amurka da Japan kowa ne ya dauki kashi 20%. A hakika dai, shekaru 10 masu zuwa, za su kasance lokacin zinare na sabon zagaye na ci gaban kimiyya da fasaha na zamani. Ingancin da aka samu a fannin kimiyya da fasaha kai tsaye ke tantance matsayin wata kasa a duniya.

Yanzu dai, kasar Sin ta cimma nasarar samun ci gaba ta kokarin da take yi, tare da kawar da talauci, kuma tana taka muhimmiyar rawa a wasu manyan rikice-rikicen duniya. Danniyar da Amurka ke yi ba za ta iya dakatar da saurin ci gaban kimiyya da fasaha na kasar ba, har ma za ta karfafa niyyarta a fannin yin kirkire-kirkire da kanta. (Bilkisu Xin)