logo

HAUSA

Ga yadda ‘yan jihar Xinjiang suke noman auduga cikin shirin bidiyo da wani dan Isra’ila ya dauka a Xinjiang

2021-04-09 16:45:15 CRI

Ga yadda ‘yan jihar Xinjiang suke noman auduga cikin shirin bidiyo da wani dan Isra’ila ya dauka a Xinjiang_fororder_微信图片_20210409163804

Kwanan nan ne na kalli wani shirin bidiyo da wani dan kasar Isra’ila mai suna Raz Galor, ko kuma Gao Yousi a yaren Sin ya dauka, game da ziyarar gani da ido da ya yi a birnin Aksu na jihar Xinjiang. Dalilin zuwansa Xinjiang shi ne, amsa tambayar da abokanansa dake kasashen waje suka yi masa, dangane da ainihin halin da ake ciki a Xinjiang. Kamar shin da gaske ne ana tilastawa ‘yan kwadago su yi aikin noman auduga a wajen? Shin da gaske ne ana muzgunawa ma’aikata ‘yan kananan kabilun wajen?

A bidiyon da ya dauka, na ga Mista Raz ya je wata gonar noman auduga, inda ya hau motar shuka irin audugar don gwadawa. Abun da ya ba shi mamaki a nan shi ne, motar tana sarrafa kanta ne, ba tare da direba ba, har ma ana iya amfani da wayar salula don sarrafa motar. Har wa yau, Raz ya nuna mana yadda ake amfani da na’ura ta zamani don tsinkar auduga, gami da karamin jirgi maras matuki na fesa maganin kashe kwari a gonaki.

A bidiyon kuma, wani mai gonar auduga ya shaidawa Raz cewa, ya yi hayar wasu ma’aikata 15 don aikin noman audugar a gonakinsa, da fadinsu ya zarce murabba’in mita dubu 650, kuma albashin kowane ma’aikaci ya kai kudin Sin Yuan 150 zuwa 200, kwatankwacin Naira 8700 zuwa 11500 a kowace rana. Jama’a, albashi nawa kuke samu a kowace rana a Najeriya?

Ina fatan za ku fahimta, a gonakin auduga masu fadi haka, ma’aikata 15 ne kacal suke aiki, wato akasarin ayyukan noma, injuna masu sarrafa kansu ne ke yi, kuma kowace rana ma’aikatan za su samu albashi mai tsoka, ina bukatar gwamnatin kasar Sin ta tilasta musu aiki? Ina dalilin da ya sa ake muzguna su?

Ga yadda ‘yan jihar Xinjiang suke noman auduga cikin shirin bidiyo da wani dan Isra’ila ya dauka a Xinjiang_fororder_1

Wannan bidiyon da Raz Galor ya dauka a Xinjiang, ya sa na tuna da wani bidiyon na daban da na taba kallo, inda wani matashin kasar Amurka bakar fata, ya ce a lokacin da yake aji na uku a makarantar firamare dake jihar Alabama, wata rana mai zafi, malamansu sun kai shi da abokan karatunsu zuwa wata gonar noman auduga mai nisan gaske, don su diba auduga. Amma bayan da yaran suka gama aikin, ana daukar dukkan audugar da suka diba, babu komai da ya rage musu, komai wahalar da suka sha. Tambayata a nan ita ce, ko wannan malamin jihar Alabama ta kasar Amurka shi ne ya yi amfani da kwadago yara? Har ma bai biya su kome ba bayan sun yi aiki?

Mahukunta a jihar Xinjiang ta kasar Sin sun bayyana cewa, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, sun gayyaci kafafen watsa labaran kasashen yammacin duniya, ciki har da BBC, su zo Xinjiang don yin ziyarar gani da ido gami da ruwaito rahotanni. Kafafen yada labaran sun ziyarci masallatai, da cibiyar karatun Alkur’ani mai girma ta addinin Musulunci, da cibiyar horas da ma’aikata, har da wuraren aiki na al’ummomi daban-daban a jihar, amma ina dalilin da ya sa suka kirkiro labaran bogi bayan da suka kammala ziyararsu a Xinjiang?

Dalilin kuwa shi ne, kasashen yammacin duniya ba su son ganin ci gaban kasar Sin da sauri haka, suna son amfani da batun Xinjiang don shafawa gwamnatin kasar Sin bakin fenti, da hana ci gaban sana’ar noman auduga ta Xinjiang, wadda ta kasance jigon tattalin arzikin wajen.

Na karanci wasu sakwannin da mabiyana a shafin sada zumunta ta Facebook suka turo mini, inda wasu suka nuna goyon-bayansu ga gwamnatin kasar Sin, wasu kuma suka tambaye ni, mene ne ainihin halin da ake ciki a Xinjiang? Malam bahaushe kan ce, gani ya kori ji, kuma rashin sani ya fi dare duhu. Ina gayyatar ku zo jihar Xinjiang ta kasar Sin, jiha ce mai albarka da son karbar baki, mu ziyarta tare, ta yadda za mu ganema idanunmu ainihin abun dake faruwa, kamar yadda dan Isra’ilar Mista Raz Galor ya yi! (Murtala Zhang)