logo

HAUSA

Ta yaya aka fitar da “kankara mafi sauri”

2021-04-09 16:16:28 CRI

Daga cikin gidajen wasannin kankara na gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da za a shirya a birnin Beijing a shekara mai zuwa, gidan wasan gudun kankara cikin sauri shi ne sabon gidan wasa daya kacal da aka gina. A gwajin wasanni da ake gudanarwa a kwanan nan, an kuma gudanar da gasa a karo na farko a gidan wasan, wanda ke dukufa a kan fitar da “kankara mafi sauri”. Amma ta yaya ne ake fitar da “kankara mafi sauri”, yaya kuma harkokin gwaji suke gudana?

Ta yaya aka fitar da “kankara mafi sauri”_fororder_微信图片_20210409153736

A ranar 7 ga wata, an yi wa filin kankara na gidan wasan gudun kankara cikin sauri gwaji, filin da fadinsa ya kai muraba’in mita dubu 12, wanda ya kasance filin kankara mafi fadi a nahiyar Asiya, inda ’yan wasa suke gudun kankara da saurin da ya kai kimanin kilomita 60 cikin sa’i daya. Kasancewarta darektar kula da wasan gudun kankara cikin sauri, Madam Wang Beixing, wadda ta taba samun lamba ta biyu a gasar Olympics ta lokacin hunturu, ta ce, bisa gwajin da aka yi, ‘yan wasa sun nuna yabo ga filin wasan. Ta ce,“Gaba daya za mu shafe kwanaki hudu muna gudanar da wasa ta fannoni 14, wanda ya kasance iri daya da na gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu. Kafin mu fara gasar, ni da mataimakina duk mun yi gwaji a kan kankara. A gani na, filin kankara ya yi kyau, duk da cewa akwai wasu matsaloli kalilan da muka bayyana wa masaninmu mai suna Mark, wanda ke kula da samar da kankara, matsalolin da galibinsu suke shafar ’yar gargada da aka gano.”

Ta yaya aka fitar da “kankara mafi sauri”_fororder_微信图片_20210409153819

Mark, wanda ya zo daga kasar Canada, yana kula da samar da kankara ga gasar, kuma ya taba ba da gundummawar samar da kankara a gasannin wasan Olympics na lokacin hunturu guda biyar da aka shirya a baya, don haka ya goge a wannan fanni. A wannan karo, yana kula da samar da kankara a gidan wasan gudun kankara cikin sauri, a game da wannan sabon gidan wasa da aka gina tare da yin la’akari da kiyaye muhalli da inganci, yana mai cewa,“An samar da kankara ne da ruwa, kuma an mai da hankali a kan kiyaye muhalli musamman ta fannin tsarin samar da kankara, wato ana amfani da sinadarin Carbon Dioxide wajen samar da kankara, wanda ke iya kiyaye muhalli, kuma ta hanyar yin amfani da Carbon Dioxide, an kara inganta aikin samar da kankara, wanda abu ne mai kyau gare mu.”

Burin da ake neman cimmawa wajen gina gidan wasan gudun kankara shi ne samar da “kankara mafi sauri” ga ’yan wasan. Mataimakin manajan kula da gidan, wanda kuma shi ma yake kula da aikin samar da kankara, Mr. Feng Gang ya ce, ana iya kayyade bambancin zafin kankara da ake samarwa da sinadarin Carbon Dioxide cikin digiri 0.5, wanda abu ne da ba za a iya cimmawa ba ta yin amfani da sauran sinadarai na samar da kankara. Ya ce,“Taushin kankara zai bambanta bisa ga bambancin zafinsa. In dai an samu bambancin zafin kankara, lalle za a samu wasu sassa na filin kankara da ke da taushi, inda zai rage saurin gudun ’yan wasan, a yayin da a wasu sassa kuma, kankara zai yi tauri, wanda zai haifar da matsala ga ’yan wasa. Amma idan an samar da kankara ba tare da mabambantan zafi, lalle ’yan wasan za su ji daidai a duk inda suke.”

Ta yaya aka fitar da “kankara mafi sauri”_fororder_微信图片_20210409153830

Madam Wang Beixing ta ce, ’yan wasan gudun kankara da malaman wasan na duk duniya na mai da hankali a kan gwajin da ake yi, kuma su a nasu bangaren suna kokarin bayyana wa takwarorinsu sakamakon gwajin da aka gudanar. Ta ce,“Mun tarbi wakilan kungiyar ’yan wasan gudun kankara ta duniya a watan Nuwamban bara, wadanda suka nuna amincewa da gidan wasan da yadda aka shirya gasar, da ma hidimomin da ake samarwa. A gwajin da muke gudanarwa a wannan karo, mun kuma aika musu da bidiyo na kai tsaye. Muna shirya komai da komai bisa dokokinsu da ka’idojinsu, shi ya sa suka gamsu sosai.” (Lubabatu)