logo

HAUSA

An kaddamar da manyan ayyukan da aka zubawa jarin yuan biliyan 72 a Xinjiang

2021-04-08 14:28:19 CRI

An kaddamar da manyan ayyukan da aka zubawa jarin yuan biliyan 72 a Xinjiang_fororder_210408-changji

A ranar 6 ga wata, aka kaddamar da kashi mafi yawa na ayyukan da za su lakume jarin yuan biliyan 72.027 a Xinjiang, wandanda suka shafi bangarorin makamashi mai tsafta da man fetur da albarkatunsa da wutar lantarki da nazarin magunguna da al’adu da yawon bude ido da sauransu.

Rahotanni sun bayyana cewa, dukkan ayyukan sun shafi manyan gine-gine da za a yi a yankin Changji na kabilar Hui mai cin gashin kai ta jihar Xinjiang. Wannan mataki ya kaddamar da fara ayyukan gine-gine a yankin Changji a 2021. A bana, yankin Changji ke shirin fara ayyuka 202 da za su lakume jarin yuan biliyan 111.402. (Fa’iza Mustapha)