logo

HAUSA

Birnin Wuhan Ya Yi Matukar Sauyawa Shekara Guda Bayan Kullen Sama Da Kwana 70

2021-04-08 17:18:25 CRI

Birnin Wuhan Ya Yi Matukar Sauyawa Shekara Guda Bayan Kullen Sama Da Kwana 70_fororder_0408-1

Tun da sanyin safiya a birnin Wuhan, fadar mulkin lardin Hubei na tsakiyar kasar Sin, ana iya ganin masu sayar da abinci na sauke kayan bukatun sana’arsu. A lokacin cin abincin rana kuwa, ma’aikata kan cika wuraren kalaci. Can da yamma kuma, tsofaffi da masu matsakaitan shekaru na turuwa zuwa filayen raye-raye, suna gwada fasahohinsu daura da kogin Yangtze.

Yanzu haka shekara guda ke nan, bayan da aka kawo karshen zaman kulle da al’ummar birnin Wuhan kimanin miliyan 11 suka shiga a karo na farko, tare da farfado da harkokin rayuwa na yau da kullum a birnin, sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19.

Duniya ta yi matukar mamakin dakatar da zirga zirgar jiragen sama, da na kasa, har ma da motocin zirga zirgar al’umma a ciki da wajen birnin Wuhan. Ko shakka babu, daukar wannan mataki na dakatar da zirga zirga, da sanya marufin baki da hanci, da gaggauta gina asibitocin wucin gadi a birnin, sun ja hankalin duniya. Kuma masanan lafiya da na kimiyya, musamman na kasar Sin, sun goyi bayan wadannan matakai a wancan lokaci, a kokarin da ake yi na dakile bazuwar cutar zuwa sauran al’ummun kasar Sin, har ma da sauran sassan duniya.

A daya hannun kuma, kasar Sin ta gabatar da shawarwari ga hukumar lafiya ta duniya WHO, dangane da dabarun da take dauka na shawo kan wannan annoba a cikin gida, ta yadda sauran kasashe ma za su yi koyi da hakan, don cimma nasarar dakile bazuwar ta a sauran sassan duniya baki daya.

Duk da wadannan matakai, wasu sassan duniya sun yi watsi da wadannan shawarwari na Sin, tare da siyasantar da batun annobar. Wasu masana da masu fashin baki na da ra’ayin cewa, da a ce sauran kasashen duniya su dauki matakai makamantan wadanda aka dauka a birnin Wuhan shekara guda da ta gabata, da ko shakka babu, da an kaucewa fadawa halin da aka shiga a yanzu, na rasa rayuwa masu tarin yawa, da durkushewar tattalin arziki.

Bayan fara gudanar da rigakafin cutar ta COVID-19 a sassan duniya daban daban, yanzu haka an fara hangen nasarori na raguwar bazuwar cutar a wasu sassa, ko da yake dai har yanzu “da sauran rina a kaba”, ta fuskar samun isassun rigakafin da duniya baki daya ke bukata.

Hakika “kwalliya ta biya kudin sabulu” a Wuhan, domin kuwa dukkanin matakan kandagarki da na jinya, zuwa na rigakafi, sun haifarwa birnin da ma kasar Sin baki daya “da mai ido”, domin kuma birnin Wuhan ya kubuta daga wannan cuta, kana harkoki sun komo yadda aka saba, cike da sauyi mai matukar ban mamaki, shekara guda bayan kullen sama da kwanaki 70 da birnin ya sha.   (Saminu)