logo

HAUSA

Jihar Xinjiang ta kasar Sin na more ci gaba da kwanciyar hankali

2021-04-08 14:22:01 CRI

Jihar Xinjiang ta kasar Sin na more ci gaba da kwanciyar hankali_fororder_210408-Xinjiang

An bayyana jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, dake arewa maso yammacin kasar Sin a matsayin wadda ke more yanayin ci gaba da kwanciyar hankali da ba ta taba samu ba a tarihi.

Mataimakin shugaban gwamnatin jihar, Erkin Tuniyaz ne ya bayyana haka, inda ya ce wasu mutanen duniya dake da wata manufa, na watsi da yadda rayuwar jama’ar Xinjiang ta kyautatu, inda suke yada jita-jita da gangan game da abubuwan da suke kira da “tilasta kwadago” da “tilasta tsarin iyali ” da “kisan kare dangi”.

A cewarsa, wasu ’yan siyasar kasashen yamma sun gwammace su aminta da karairayin da wasu masu adawa da Sin suka kitsa, maimakon sauraron buri daya na al’ummun kabilun jihar Xinjiang da yawansu ya zarce miliyan 25 da kuma gaskata yanayin ci gaba da kwanciyar hankali da Xinjiang ke ciki.

Ya ce abun da suke yi shi ne, kirkiro wasu batutuwa da suka shafi Xinjiang, da tarnaki ga tsaro da zaman lafiyan yankin, da kuma kawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin.

Jami’in ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci ga wata kafar yada labarai ta kasar Australia, yayin wata tattaunawa ta bidiyo ta hadin gwiwa da jihar Xinjiang ta dauki nauyi tare da ofishin jakadancin Sin dake Australia. (Fa’iza Mustapha)