logo

HAUSA

Sai An Zubar Da Ruwa A Kasa Kafin A Taka Damshi

2021-04-07 17:38:06 CRI

Kowa ya yi da kyau, zai ga da kyau. Duniya dai ta kalli irin rawar da kasar Sin ta taka wajen tsame al’ummarta daga kangin talauci, bayan jerin matakai da shirye-shirye da mahukuntan kasar suka dauka, har ya kai kasar ga cimma wannan gagarumar nasara, abin ke da zama wani abin al’ajabi da ba a taba gani irinsa ba a tarihin duniya. Idan ka ga wane aka ce ba banza ba.

Wannan ne ma ya sa ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar ta Sin, ya fitar da takardar bayani game da aikin da gwamnati ke yi na rage talauci a kasar. Ita dai wannan takarda mai taken "Rage talauci: kwarewar kasar Sin da gudummawar da ta bayar a wannan fanni”, ta fayyace bayanai game da hanyar da Sinawa suka bi, wajen cimma muhimmiyar nasarar kawar da matsanancin talauci, da gabatar da salon kasar Sin, tare da raba kwarewarta, da matakai na yaki da fatara.

Baya ga budewa da kuma bangaren rufewa, takardar ta kunshi wasu sassa 5: Ciki har da babi game da muhimmin alkawarin JKS, da babi game da nasarar yaki da matsanancin talauci, da babi kan dabarun tunkarar kebabbun sassan rage talauci, da na gano sabbin hanyoyin rage talauci, da na aikin dake gaban daukacin bil adama game da samar da al’umma mai makomar bai daya wadda za ta kubuta daga fatara.

Kaza lika takardar ta tabo batun cika shekaru 100 da kafuwar JKS a wannan shekarar da muke ciki, jam’iyyar da ta kasance jigon duk wani ci gaban kasar, wadda kuma ta hade wuri guda, tare da jagorantar Sinawa, a yakin da suke yi da fatara cikin yakini, da aniyar cimma nasara a duk tsawon wannan karni.

Nasarar kasar Sin wadda ke da kaso daya bisa 5 na daukacin yawan al’ummun duniya, wajen yakar matsanancin talauci daga dukkanin fannoni, wata muhimmiyar nasara ce a tarihinta, da ma tarihin bil adama baki daya. Yabon gwano, ya zama dole. Wannan nasara da kasar Sin ta samu, wata babbar gudummawa ce ga kokarin da ake yi na kawar da kangin talauci a duniya.

Yanzu haka, al’ummar Sinawa sun yi adabo da kangin talauci tare da samun rayuwa mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, amma hakan bai hana mahukuntan kasar Sin ba da taimako iri daban daban ba ga kasashe da kungiyoyi sama da 160, dake yankunan Asiya, da Afirka, da Latin Amurka, da Caribbean, da nahiyar Oceania da kuma Turai da sauransu, ta yadda, su ma kasashe masu tasowa za su cimma burin samun ci gaba kamar yadda MDD ta tsara, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.

Masana na fatan, nasarar da kasar Sin ta samu a wannan fanni, zai kai ga yakar kangin talauci baki daya a fadin duniya, ta yadda al’ummar duniya gaba daya, za ta rayu cikin walwala da wadata. Fata na gari ake ce lamiri. (Ibrahim Yaya)