logo

HAUSA

Masanin Zimbabwe: Ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin rage talauci na Sin

2021-04-07 11:10:57 CRI

Masanin Zimbabwe: Ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin rage talauci na Sin

Jiya Talata 6 ga watan nan, ofishin yada bayanai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da aikin da gwamnati ke yi na rage talauci a kasar, lamarin da ya yi matukar jawo hankalin masanan kasashe daban daban, inda da dama ke ganin cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako wajen rage talauci, wanda zai taka babbar rawa a aikin rage talauci a fadin duniya, da kuma ci gaban bil Adama, don haka ya dace a yi koyi da fasahohin da kasar ta Sin ta samu a wannan bangaren.

Sheihun malami a cibiyar nazari, da cudanyar tattalin arziki da al’adu tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a kasar Zimbabwe Donald Rushambwa, ya jinjinawa sakamakon da kasar Sin ta samu a bangaren rage talauci matuka, inda ya bayyana cewa, sakamakon da kasar Sin ta cimma zai samar da fasahohin rage talauci masu ma’ana ga kasashe masu tasowa ciki har da kasarsa ta Zimbabwe.

Donald Rushambwa ya taba yin karatu a matakin digiri na biyu a kasar Sin tsakanin shekarar 2014 zuwa ta 2019. Yayin karatunsa a kasar, ya taba ziyartar lardunan Zhejiang da Jiangsu da Gansu da Liaoning, da ma sauran sassan fadin kasar Sin, inda ya ganewa idanun sa irin manyan sakamakon da kasar Sin ta samu kai tsaye wajen kawar da talauci, a cewarsa:“Kasar Sin ta samu manyan sakamako a fannin yaki da talauci, kuma al’ummun Sinawa da yawan gaske sun kubuta daga kangin talauci, kuma abu mafi burgewa shi ne, a kauyukan kasar Sin, kananan gwamnatocin kasar sun kara karfafawa manoma gwiwa domin su yi aiki a birane, ta yadda za su samu karin kudin shiga, tare kuma da kyautata rayuwar iyalansu. Kuma gwamnati ita ma ta samar da guraben aikin yi a kauyuka. Alal misali, akwai aikin kare gandun daji, matakin ba ma kawai samar da guraben aikin yi ga manoma yake yi ba, har ma yana cimma burin kiyaye muhalli, saboda kyautatuwar muhalli kuma na taimakawa aikin rage talauci.”

Rushambwa ya kara da cewa, aikin rage talauci da ake gudanarwa a kasar Sin, ya samar da fasahohi masu daraja ga Zimbabwe, a don haka ya dace kasar ta koyi fasahohin kasar Sin, ta yi amfani da fifikon arzikin albarkatun ‘yan kwadago, ta kara zuba jari a fannonin aikin gona, da ba da ilimi da sauransu, ta yadda za ta cimma burin rage talauci a kasar, yana mai cewa,“Ina ganin cewa, kasashe masu tasowa, kamar kasarmu Zimbabwe, suna da arzikin albarkatu iri daban daban, musamman ma wajen ‘yan kwadago, amma ba su yi amfani da su yadda ya kamata ba. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, abu mafi muhimmanci yayin da ake kokarin yaki da talauci shi ne, masu fama da talauci su yi aiki tukuru bisa dogaro da kansu, ta yarda da ra’ayin sosai, ya kamata a yi kokari tare domin rage talauci. Hakika aikin gona muhimmin aiki ne da ake gudanarwa a Zimbabwe, domin samun ci gaban tattalin arzikin kasar, amma manoman kasarmu ba su da isasshun kudin sayen irin hatsi, da takin zamanin da suke bukata, kana yaran kasarmu suna bukatar koyon ilmomi, shi ya sa akwai bukatar kara zuba jari kan aikin ba da ilmi, duk wadannan za su taimakawa aikin yaki da talauci a kasarmu.”

Haka zalika, Rushambwa shi ma ya gabatar da shawarwari, game da rage talauci a kasashen Afirka, ciki har da kasarsa ta Zimbabwe, inda ya bayyana cewa,“Akwai albarkatu na arziki a kasashen Afirka, amma kasashen nahiyar na fama da matsalar karancin fasahohin amfani da wadannan albarkatu. A don haka suke bukatar kasashen duniya su zuba jari. Hakika kasar Sin ta riga ta samar da tallafi da goyon baya mai nasaba da hakan.

Alal misali, kasar Sin tana taimakawa kasashen Afirka, wajen gina manyan kayayyakin more rayuwar jama’a, kuma tana gudanar da hadin gwiwar cinikayya tsakaninta da kasashen Afirka, inda har ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta kasashen nahiyar Afirka. Duk wannan kokari da kasar Sin take yi, sun sa kaimi ga ci gaban zamantakewar al’umma, da tattalin arzikin kasashen Afirka matuka. Suna kuma ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu, wato Sin da Afirka gaba yadda ya kamata.”

Ban da haka, Rushambwa ya bayyana cewa, wata kila annobar cutar numfashi ta COVID-19 da take bazuwa a fadin duniya, za ta jefa karin al’ummomin kasashen duniya cikin mawuyacin yanayi, amma duk da haka a yanzu, kasar Sin ta gabatar da shawarwarin kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen kardagarkin annobar, domin dakile yaduwar ta cikin gaggawa. Yana mai cewa, matakan da kasar Sin ta dauka, za su ba da gudummowa ga farfadowar tattalin arzikin duniya. (Jamila)