logo

HAUSA

Rahoton WHO ya bayyana cewa ba zai yiyuwar bullar kwayoyin cutar COVID-19 daga dakin gwaje-gwaje ba

2021-04-07 09:24:02 CRI

A kwanakin baya ne, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar da rahoton binciken gano asalin cutar COVID-19 a duniya, biyo bayan kammala aikin binciken hadin gwiwa da ta gudanar da kasar Sin, kan wasu batutuwa, ciki har da hanyoyin da kwayar cutar take bi da makomar binciken a sauran kasashe.

Rahoton WHO ya bayyana cewa ba zai yiyuwar bullar kwayoyin cutar COVID-19 daga dakin gwaje-gwaje ba_fororder_210407-世界21012-hoto1

Baki daya, masana 34 daga WHO da kasar Sin ne, suka gudanar da binciken hadin gwiwa na kwanaki 28, daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu a birnin Wuhan na kasar Sin. Yayin aikin binciken, masanan sun mayar da hankali ne, wajen gano yiwuwar hanyar da cutar ta bi har ta bulla.

A cewar rahoton, bullar COVID-19 ta wata hanyar wani abu mai rai, “abu ne da ake ganin yiwuwarsa”. Sannan bullar cutar ta hanyar daskararren abinci “na iya yiwuwa”, kana bullar cutar bisa kuskure daga dakin bincike, “akwai shakku kan aukuwarsa.”

Haka kuma, masanan sun gabatar da jerin shawarwari game da gudanar da bincike a nan gaba: yadda za a tsara cikakken rumbun adana muhimman bayanai, da gudanar da karin bincike kan cututtuka cikin sauri da wuraren da ake ganin sun bulla, da yin sharhi kan irin rawar da wuraren adana daskarren abinci ke takawa kan yiwuwar bulla da yaduwar kwayar cuta.

Rahoton WHO ya bayyana cewa ba zai yiyuwar bullar kwayoyin cutar COVID-19 daga dakin gwaje-gwaje ba_fororder_210407-世界21012-hoto2

Kasar Sin ta yi imanin cewa, binciken hadin gwiwar, ya taka gagarumar rawa wajen yayata hadin gwiwar kasa da kasa wajen gano asalin COVID-19. Ta kuma yi watsi da sanarwar hadin gwiwar Amurka da wasu kasashe 13, wadda a cikin ta, hadakar kasashen suka ce wai, sun damu game da abun da yake kunshe cikin rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO, game da sakamakon binciken da aka gudanar, na gano asalin cutar COVID-19 a duniya.

Wannan sanarwa ta nuna yadda wasu kasashe ke wulakanta kimiyya, suna siyasantar da binciken da ake yi game da asalin wannan cuta.

Sanin kowa ce cewa, aikin binciken asalin kwayar cutar COVID-19, batu ne da ya shafi kimiyya, wanda kuma ya dace masana a fannin daga dukkanin duniya, su ba da gudummawar cimma nasararsa. Bai kuma kamata a siyasantar da shi ba. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)