Ta yaya za a taimakawa yara su nisanci wayar salula?
2021-04-06 17:28:58 cri
Na kan ji mutane dake kusa da ni suna cewa:
"Lokacin da muke kuruciya, ba mu da kayan lantarki, duk da haka muna farin ciki sosai a lokacin, manya da yara ma suna farin ciki sosai. Farin ciki na hakika da ake samu a cikin iyali. Amma, yanzu yanayin ya canja.”
“Ban san me ke faruwa ba, yanzu yara kamar aljanu suke, da zarar sun fara amfani da wayar salula, ba sa kaunar su daina. Har suna musu da iyayensu, saboda kawai su yi wasa da wayar salula, sun fi son zama da salula fiye da iyayensu.”
Wata manufar da ma'aikatar ilimi ta kasar Sin ta fito da ita a farkon watan Maris da muke ciki, game da "Sanarwar karfafa yadda daliban makarantun firamare da na sakandare za su rika amfani da wayar salula ga daliban”, inda ta bukace su, da kada su zo makaranta da wayar salula, don magance mummunan sakamakon da amfani da salula da sauran kayayyakin laturoni fiye da kima zai haifar.
An gabatar da irin wadannan manufofi na hana amfani da wayar salula tsakanin dalibai a kasashe da dama, saboda sha’awar da yaran ke da ita na yin wasa da wayar salula sosai, wannan ta zama wata matsala a duniya baki daya. Amma, duk da tsauraran ka'idodi daban-daban da aka bullo da su, a wasu lokutan yara suna wasa da salula a boye, inda suke daukar wayoyin salula ba tare da sanin iyayensu ba.
Abu na farko da ya kamata mu fahimta shi ne, me ya sa yara suke son yin wasa da salula sosai? Shin laifin salular ce? Mai Ilimin falsafal nan Karl Marx ya taba bayyana cewa: Wasu dalilai na boye na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban abubuwa, kana dalili na fili, sharadi ne kawai na haifar da abubuwan kawai. Don haka, akwai wasu dalilai na boye dake sanya yara son yin wasa da salula,
Da farko, shi ne rashin sha’awar yin karatu.
Idan yaro ba ya son tafiya makaranta, kuma ba ya jin dadi a yayin da yake karatu a makaranta, to akwai yiwuwar zai nemi wasu abubuwa masu ban-sha’awa a yanar gizo. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, daliban makarantar firamare da na sakandare wadanda suka gaji da karatu, sun fi iya wasan fada na yanar gizo. Masu tsara wasannin na yanar gizo sun san yadda za su jawo hankalin yara, inda aka tsara hanyoyi iri daban-daban, ciki har da kara kammala ayyuka, neman karin matsayi, da ba da kyautan abubuwa da dai sauransu, sun sanya yara farin ciki da ba su taba samu ba a duniyar zahiri.
Baya ga wasanni na yanar gizo kuma, akwai kuma littattafan labari da aka wallafa a yanar gizo, wadanda kullum ake sanya wasu abubuwa na jiran tsamani, kuma ake sabuntawa lokaci lokaci, don yaudarar yara da labarai masu ban sha'awa. Yara ba su da zurfin tunaninsu, don haka, da wuya su iya bijirewa wadannan sabbin abubuwa, kuma nan da nan za su iya fadawa tarkon da ba za su iya fita ba.
Idan yara sun gaji da karatu, akwai bukatar iyaye su rika taimaka musu, ta yadda za su kyautata rayuwarsu da ma harkokinsu na makaranta. Kowane yaro yana da nasa halin na musamman, Ba a taru aka zama daya ba. Kowane yaro da akwai fannin da ya kware, ya kamata iyaye su gano fannonin da ’ya’yansu suka kware, su rika yi musu jagora daga lokaci zuwa lokaci. Idan yara ba su samu maki mai kyau a karatu ba, ya kamata iyaye su rika karfafawa 'ya'yansu gwiwa, ta yadda za su shiga wasu wasannin motsa jiki da ayyukan kwadago da ayyukan fasaha da makaranta take shiryawa, ta haka yara za su iya sake jin dadin shiga makaranta, kuma watakila za su yi watsi da duniyar yanar gizo.
Wani dalili na biyu na boye da suke sanya yara son yin wasa da salula, shi ne, ba a biya musu bukatunsu na tuntubar mutane.
Kowane yaro yana da bukatun tuntubar mutane, kuma a yayin da suke girma, za su gina wata kamarar duniya ce kawai bisa tunaninsu. Idan yaro ba ya iya samun abokai a cikin duniya ta zahiri ba, kadaici da suke ji cikin zuciyarsa zai haifar musu da matsala da za ta iya shafar rayuwarsu.
Amma a cikin duniyar wasa, muddin kana da kwarewa sosai, to akwai wasu da za su nuna maka yabo, da kuma zura maka ido. Yara za su iya samun kansu cikin duniyar wasa, kuma wasu abokansu, za su iya jan hankalinsu, daga karshe su rude su, har su manta da abubuwa masu kyau dake faruwa a duniya ta zahiri.
Watakila wasu yaran da ba sa ma'amala da jama'a ne, saboda halinsu. Kuma kadaici na iya haifar da yawan bacin rai, amma a hakika ko wane yaro ko yariniya na sha’awar yin ma’amala da wasu. Don haka, ya kamata iyaye su rika yin hakuri sosai don wayar da kan ‘ya’yansu, bari su bude zuciyarsu ga abokansu game da duniyar zahiri, hakan zai ba su damar yin cudanya da abokansu a zahiri, har ma su samu kwanciyar zuciya.
Boyayyen dalili na uku da suka sanya yara son wasa da salula shi ne, tasirin iyayensu a kansu.
Iyaye da yawa suna korafi game da yadda yaransu suke wasa da salula, amma kamata ya yi su ma iyayen su dubi kansu: Ko ina amfani da salula a gaban ‘ya’yana? Ko ina nuna wa 'ya'yana misali mai kyau? Tabbas, iyaye da yawa za su karyata wadannan tambayoyi: A galibin lokuta, mu iyaye muna amfani da salula ne don aiki, amma yara su kan yi amfani da salula domin wasa kawai. Ta yaya za a kwantanta a tsakaninmu da ‘ya’yanmu?
Kamar yadda kowa ya sani, duk abin da iyaye suka fada ko suka aikata yana tasiri ga ‘ya’yansu sannu a hankali. A yayin da ‘ya’yansu ke kanana, idan sun ga iyayensu suna wasa da salula, to, su ma za su yi sha’awar yin haka. Idan kuma iyaye suna amfani da salula na dogon lokaci, kuma ba su da lokacin kula da yaransu, to yaransu ba za su ji dadin da iyalinsu ba a yayin da suke girma.
Shirin "Muryar matasa", wani shirin bidiyo ne da ya shahara a nan kasar Sin, wanda ke mayar da hankali kan lafiyar tunanin matasa, inda matasa ke gabatar da bukatunsu ko kuma rashin gamsuwa ga iyayensu, malamansu, makarantunsu da ma al’ummar kasar. A cikin shirin, akwai wani dalibi mai suna Ye Zijian ya bayyana yana kuka cewa,
“Lokacin da nake karami, na yi tunanin cewa, salula su ma 'ya'yan iyaye na ne. A duk lokacin da na daga kai don na gan su, a ko da yaushe suna duba salula ne kawai. Kuma idan sun bukaci na yi shiru ko kar na dame su, to sai su jefa min salula, don in yi wasa ni kadai.”
Sabili da haka, lokacin da muke gunaguni game da wasa da salula da ‘ya’yanmu suke yi, to ya kamata mu fara duba kanmu kafin mu yi maganar yara.
Kamar wata malamar dake aiki a jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing Wang Jia ta bayyana,
“Iyali ita ce makaranta ta farko a rayuwa, kuma iyaye su ne malaman farko na yaransu. A zamanin da muke ciki na yanar gizo ta tafi da gidanka,ga kuma yawaitar amfani da wayar salula, dole ne iyaye su yi kokarin kara yadda suke baiwa ‘ya’yansu a gida, da kuma hada kai tare da makaranta don jagorantar ‘ya’yansu wajen kafa kyakkyawar dabi'ar amfani da wayar salula yadda ya kamata, hakan zai sa iyaye daukar nauyin dake wuyansu na yiwa ‘ya’yansu tarbiyar da ta dace, baya ga kara samun hikima.”