logo

HAUSA

Kallo Ya Koma Sama

2021-04-05 19:54:58 CRI

Kallo Ya Koma Sama_fororder_0405-2

Masu azancin magana na cewa, “kallo ya koma sama wai shaho ya dau giwa.” Tauraron kasar Sin na kara haskawa a idanun masana tattalin arzikin duniya tun bayan nasarar da kasar ta samu na kawar da kangin talauci a tsakanin al’ummarta inda masu fashin baki ke bayyana nasarar da Sin ta samu a fagen yaki da talauci a matsayin wani muhimmin darasi da ya kamata duk duniya ta kalla domin daukar izina. Ko shakka babu, matakan da gwamnatin Sin ta dauka karkashin jagorancin jam’iyyar JKS a bayyane take ya haifar da babban sakamako wanda duk duniya ke yin Allah sam barka. Hakika, yaki da fatara a tsakanin al’umma tamkar wani shiri ne na shimfida zaman lafiya a tsakanin kowace al’umma, domin kuwa, yayin da al’umma ke cikin rufin asiri da zaman wadata babu sauran batu na neman ta da zaune tsaye domin kowa yana himmatuwa ne wajen fadi tashin yadda zai kare mutuncinsa da na iyalansa. Batun nasarorin da kasar Sin ta samu wajen raba al’ummarta daga kangin talauci musamman a ’yan kwanakin baya bayan nan ya zama babban jigon da ake ci gaba da tattaunawa a fadin duniya. Ko da a ’yan kwanakin da suka gabata ma, wani babban masanin tattalin arziki na MDD, Elliott Harris, ya ce nasarar da kasar Sin ta samu wajen kawar da kangin fatara babban abin koyi ne ga duniya baki daya. Harris ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a tattaunawar da ya yi ta kafar Email cewa, wannan muhimmin darasi ne ga dukkan al’umma, domin kawar da talauci ba aiki ne da za a iya cimmawa a cikin kankanin lokaci ba, ko kuma a iya cimmawa karkashin wata manufa kwaya daya tilo ba. Lamari ne dake bukatar jajircewa ba tare da jinkiri ba, kuma batu ne dake bukatar daukar matakai masu dorewa, masanin ya bayyana nasarar yaki da talaucin na kasar Sin da cewa abin mamaki ne kuma mai karfafa gwiwa. Masanin tattalin arzikin na MDD ya kara da cewa, kasar Sin ta yi kyakkyawan amfani da damammakin da ta samu a matsayinta da wata babbar kasuwar kasa da kasa kuma abokiyar cinikayyar duniya, kana ta yi amfani da wannan dama wajen samun muhimmin sakamako. Ya ce wannan wani babban misali ne da ya kamata ragowar kasashen duniya su yi koyi. Da ma dai masu hikimar magana na cewa, “daga na gaba ake gane zurfin ruwa”. Ya kamata kasa da kasa su dauki darasi daga manyan nasarorin da Sin ta cimma a wannan muhimmin fannin na yaki da fatara domin a gudu tare a tsira tare don a samu dawwammamen zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma samun bunkasuwa da makoma mai haske ga dukkan bil Adama. (Ahmad Fagam)