Sharhi: Dasa Bishiyoyi Don samar da Kyakkyawar Makoma
2021-04-04 21:29:24 CRI
A ranar 2 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dasa bishiyoyi tare da wasu mazauna birnin Beijing, inda ya yi kira da a yi kokarin samun daidaituwa a tsakanin dan Adam da muhallin halittu, yayin da ya sake jaddada aniyar kasar Sin kan bin hanyar samun bunkasuwa mai inganci ba tare da gurbata muhalli ba. Ko da yaushe Shugaba Xi yana dora matukar muhimmanci kan kiyaye muhalli. Yadda yake dasa bishiyoyi a jerin shekaru tara da suka gabata ya zama abin koyi ta fuskar kiyaye muhalli.
A matsayinta ta kasa mafi girma ta biyu a fannin raya tattalin arziki, yanzu Sin tana matakin samun ci gaba mai inganci, kana samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba ya riga ya zama wani muhimmin bangare na manufofin cigaban kasar, wadda ta kunshi fannonin kirkire-kirkire, daidaituwa, kiyaye muhalli, bude kofa, da ma more sakamako.
Alkaluma na nuna cewa, tsakanin shekarar 2016 zuwa ta 2020, kasar Sin ta dasa bishiyoyi mai fadin murabba’in hekta miliyan 35, yawan masu aikin sa kai na dasa bishiyoyin ya zarce biliyan 2.8, wadanda suka dasa bishiyoyin biliyan 11.6. Yadda kasar Sin ke kokarin kiyaye muhalli ya amfanawa dukkan Sinawa.
Kyakkyawan muhallin halittu shi ne abu mafi adalci ga jama’a, wanda ke iya kawo alheri ga kowanensu. Wannan ra’ayi na daga cikin babbar manufar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai mulkin kasar, wato yin kokari dari bisa dari don bautawa jama’a. A tarihin jam’iyyar na shekaru kusan 100, kyautata zaman rayuwar jama’a shi ne burinta, lamarin da ya sa kyautata muhallin halittu don biyan bukatun jama’a ya zama hanyar da take bi ba tare da kaucewa ba.
Bisa jagorancin Shugaba Xi, ana daukar batun kiyaye muhalli a wani muhimmin matsayi a cikin babban tsarin raya kasar Sin. A cikin sabon shirin da aka bayar a kwanakin baya, kasar Sin zata ci gaba da bin manufar “kyakyawan muhalli shi ne dukiyoyi”, sa’an nan ta gabatar da wasu sabbin burikan da zata yi kokarin cimmawa nan da shekaru biyar masu zuwa, kamar yawan fadin gandun dazuka a shimfide zai kai kaso 24.1 bisa dari, yawan makamashin da ake amfani da shi wajen ayyuka zai ragu da kaso 13.5, yawan gurbatacciyar iskar carbon dioxide da za a fitar zai ragu da kaso 18 da dai sauransu.
Kiyaye muhalli don tinkarar sauyewar yanayi na bukatar kokarin kasa da kasa. Ko da yaushe Sin na dukufa wajen aikin tafiyar da harkokin muhalli na duniya. A watan Oktoba mai zuwa, kasar Sin zata dauki nauyin shirya taro karo na 15 na masu daddale yarjejeniyar kiyaye nau’ikan halittu ta MDD wato COP15 a takaice. Taron wanda aka mayar da batun kiyaye muhallin halittu a matsayin babban takensa a karo na farko, zai samar da dama ga kasa da kasa wajen kokarin samun daidaituwa a tsakanin dan Adam da muhallin halittu. Lamarin kuwa da ya nuna aniyar kasar Sin ta ba da gudummawarta a wannan fanni.
Ya kamata kowa ya sauke nauyin kiyaye muhalli dake wuyansa, ganin yadda zai samu amfani daga ciki. Kasar Sin mai al’umma biliyan 1.4 na kokarin karfafa gwiwar duniya bisa matakan a zo a gani da ake dauka, lamarin da ya shaida yadda take sauke nauyi a wuyanta a matsayin wata babbar kasa a duniya.(Kande Gao daga sashen Hausa na CRI)