Kasashen yamma na nuna fuska biyu kanhakkin yada labarai cikin ’yanci
2021-04-03 15:30:07 CRI
Kwanan baya, kafar watsa labarai ta BBC ta wallafa wata sanarwa a shafinTwitter cewa, John Sudworth, wanda ake kira Sha Lei da Sinanci yaisa lardin Taiwan, a matsayinsa na ci gaba da zama walikin BBC a Sin. Ban da wannan kuma, kungiyar manema labaran ketare dake kasar Sin(FCCC), wadda ba ta samu amincewa daga kasarSin ba, kuma mambobinta bai kai rabin manemalabaran ketare dake Sin ba, sun ba da watasanarwa don zargi cewa, halin da manemalabaran ketare ke ciki a Sin ya kara tsananta. Shin ko wannan ne dalilin da ya sa John Sudworth ya bar babban yankin Sin, ko yana jinkunyar aikata abu maras kyau a babban yanki ne, shi ya sa ya gudu?
A hakika, John Sudworth ya bar babban yanki batare da sanar da jami’in dake kula da harkokinmanema labaran ketare ba, kuma bai mikatakardar barin aikinsa ba. Bisa aya ta 13 ta ka’idar hukumomin yada labarai da manemalabarai na ketare dake kasar Sin da kumatakardar ba da shawara ga manema labaranketare dake kasar Sin, kamata ya yi, wakilanketare sun mika takardar barin aikinsu kafin subar kasar. Amma, John Sudworth bai sanar da wata hukuma barinsa da mika takardar ba. Yanzuwa’adin katinsa na aikin jarida ya kare, shi bawakilin BBC a kasar Sin ba ne, saboda ya gududaga babban yanki. Amma, wannan sanarwar ta ce John Sudworth yana ci gaba da kasancewa a matsayin wakilin BBC a kasar Sin, sai dai yaketa ka’idojin kasar Sin.
Ban da wannan kuma, John Sudworth ya yiikirari cewa, duk da cewa, akwai ragowar wasuwatanni kafin wa’adin katinsa na aikin jarida yakare, amma ba shi da cikin kwanciyar hankali a Sin, abin da ya nuna cewa, halin da wakilanketare dake Sin suke ciki na kara tsananta. Amma, a hakika, wa’adin daukacin kimaninkashi 98 cikin 100 na wakilan kafofin watsalabaran ketare shekara daya ya rage. FCCC ta bada sanarwa cewa, John Sudworth da iyalansa sun dade suna rayuwa a nan kasar Sin har kusanshekaru 9, matarsa wadda ita ce ma ’yar jaridace, wa’adin katin saura shekara daya, amma ’yanjaridar kasar Sin dake Amurka, wa’adin katinsuwatanni 3 ne kawai, kuma za su biya dala 455 a kowane watanni 3 don neman tsawaita wa’adinkatin nasu, ban da wannan kuma, gwamnatinBirtaniya ta matsa lamba har ta kori sashenCGTN, wata kafar watsa labarai ta kasar Sin daga kasar Birtaniya. Saboda haka, ana iya cewa, halin da ’yan jaridun Sin dake kasashen yammake ciki, ya fi na takwaransu dake nan kasar Sin tsananta, ko da yake, ’yan jaridun Sin suna watsalabarai bisa adalci da gaskiya a duk fannoni.
Laurene Beaumond wata ’yar jaridar kasarFaransa, da ta shafe shekaru 9 tana zaune a kasarSin, ta taba ziyartar yankin Xinjiang. Hakan yasa ta wallafa wani bayani mai taken “Yadda nakalli Xinjiang ya bambanta da wasu labaran da kafofin yada labarai na kasashen yamma sukabayar”, amma a ganin wasu kafofin yada labaraina yamma, abubuwan na zahiri da LaureneBeaumond ta shaida sun zama “labaran bogi”. Shin ko ’yancin watsa labarai a ra’ayin wasukasashen yamma shi ne bari a sauya gaskiya don bata sunan kasar Sin yadda suke so, amma ba suyarda da ’yan jaridarsu sun fadi gaskiya sabodaya saba da burin siyasarsu ba? Idan mai fadarmagana wawa ne, majiyinta ba wawa ba ne, wasu kafofin yada labarai na yamma sun toshekunnewa da idanunsu, sannan ba su da masaniyakan abubuwan dake shafar kasar Sin, inda sukarika yada labaran bogi don cimma burinsu nasiyasa.
Dan jarida kamar John Sudworth marasa da’araiki, sun gudu sun bar kasar Sin domin sun yiabu maras kyau, amma hakan ba abin mamaki bane, saboda munafuncin dodo ya kan ci mai shi, Sin kasa ce dake tafiyar da harkokinta bisa doka, duk wanda ya sauya gaskiya ya mai da fari bakizai girbe abin da ya shuka.
Sin tana bude kofarta ga waje, tana maraba dazuwan kafofin yada labarai da ’yan jaridunsu a nan kasar, idan ba su son kasar Sin, to a matsayin su dan jarida, ya kamata, su mumuntaaikinsu, su rika ba da labari bisa gaskiya da adalci. (Amina Xu)