logo

HAUSA

Masanan kasa da kasa sun yabawa Sin kan nasarorin da ta samu wajen yaki da talauci ta hanyar bada ilmi

2021-04-02 14:12:57 CRI

Kawar da talauci tare da tabbatar da cewa, kowa ya samu ilmi mai inganci, su ne muhimman batutuwa biyu da suka taimaka wajen cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa na MDD. Bisa yanayin da ake ciki wato yadda ake kokarin tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta a sakamakon cutar COVID-19, zai yi wuya a cimma wadannan abubuwa biyu a duniya. A yayin taron tattaunawa mai taken bada ilmi hanya mai muhimmanci ce wajen kawar da talauci da aka gudanar a ranar 31 ga watan Maris, mahalarta taron sun yabawa kasar Sin kan nasarori da ta cimma a wannan fanni. Sun bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su yi koyi fasahohin Sin a wannan fanni.

An gudanar da taron tattaunawa na kasa da kasa mai taken bada ilmi hanya mai muhimmanci wajen kawar da talauci a zahiri da kuma ta yanar gizo tare, inda aka maida hankali ga burin samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030, da kuma tattauna alakar dake tsakanin bada ilmi da yaki da talauci. Mataimakin ministan kula da harkokin bada ilmi na kasar Sin kuma direktan kwamitin hukumar kula da ilmi, kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO na kasar Sin Tian Xuejun ya yi nuni a cikin jawabinsa cewa, Sin ta aiwatar da manufofin yaki da talauci bisa yanayin da ake ciki, da hanyar musamman da kasar ta tsara wajen yaki da talauci, da kafa tunanin musamman na yaki da talauci, daya daga cikin tunanin shi ne maida aikin bada ilmi a matsayin aikin hana yaduwar talauci da kawar da talauci da kuma samun wadata. Tian ya bayyana cewa,

“Fasahohin Sin na yaki da talauci ta hanyar bada ilmi sun shaida cewa, tilas ne a ilimantar da jama’a idan har ana so a yaki da talauci. Ilimantar da jama’a shi ne tushen kawar da talauci da kiyaye yanayin kawar da talauci, kana kawar da talauci shi ne tushen cimma burin bada ilmi nan da shekarar 2030.”

Ya kara da cewa, Sin tana son more fasahohin yaki da talauci da ta yi amfani da shi ta hanyar bada ilmi tare da ragowar kasashen duniya. Ya ce,“Gwamnatin kasar Sin tana martaba tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, musamman hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa da hukumar UNESCO, da kara nuna goyon baya ga kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa, da sa kaimi ga more fasahohin yaki da talauci ta hanyar bada ilmi domin ganin an cimma burin yaki da talauci da bada ilmi nan da shekarar 2030 a duniya baki daya.”

Shehun mlami a cibiyar nazarin aikin bada ilmi na kasa da kasa ta jami’ar Stockholm Vinayagum Chinapah ya yi nuni da cewa, Sin ba ta samu nasarorin yaki da talauci a cikin kwana guda ba, ta dauki dogon lokaci kafin ta kai ga wannan nasara. Karfin jagoranci da kiyaye zaman karko a fannin siyasa a kasar Sin, su ne muhimmin dalilin da ya sa ta samu irin wadannan nasarori. Ya ce,

“Idan hukumomin gwamnatin kasar Sin ba ta yi kokari ba, hakika Sin ba za ta iya cimma nasara da ta samu a yanzu ba, kuma kasar Sin tana son more wadannan fasahohin tare da sauran kasashen duniya. Karfin jagoranci da zaman karko a fannin siyasa da bunkasuwar tattalin arziki da manufofin nuna adalci dukkansu suna da muhummanci. Sin tana amfani da manufofin da kawo kowa zai ci moriyar samun ilmi cikin adalci don tinkarar kalubale. Kana a kasar Sin an canja tsarin bada ilmi, wato daga bada ilmi don bunkasa tattalin arziki zuwa yaki da talauci.”

Shehun malami Manzoor Ahmed na jami’ar Brac ta kasar Bangladesh yana ganin cewa, yadda kasar Sin ta kiyaye aiwatar da manufofinta yadda ya kamata na dogon lokaci, zai taimaka matuka wajen cimma burin samun bunkasuwa.

Mai bada taimako ga direktan kula da harkokin nahiyar Afirka da dangantakar kasa da kasa na hukumar UNESCO Firmin Edouard Matako yana ganin cewa, fasahohin Sin na kawar da talauci da kuma yaki da talauci ta hanyar bada ilmi, sun jawo hankalin kasa da kasa sosai, wadanda suke da babbar ma’ana ga sauran kasashe masu tasowa. Ya ce,

“Sanin kowa ne cewa, ilmi yana da muhimmanci sosai ga kokarin kawar da talauci a duniya. Ina farin cikin halartar wannan taron tattaunawa don more fasahohin Sin. Ba da ilmi don kawar da talauci, aiki ne mai muhimmanci musamman ga kasashen Afirka.” (Zainab)