logo

HAUSA

Kamfanonin kasashen waje a kasar Sin za su dandana kudarsu idan suka gudanar da ayyukansu karkashin matsin lambar ‘yan siyasar kasashen yamma

2021-04-01 21:05:00 CRI

Kamfanonin kasashen waje a kasar Sin za su dandana kudarsu idan suka gudanar da ayyukansu karkashin matsin lambar ‘yan siyasar kasashen yamma_fororder_1

Kwanan nan wani bidiyon da ya shafi aikin wata babbar motar diban auduga, a gonakin dake jihar Xinjiang ta kasar Sin ya samu karbuwa sosai a kafar sadarwar Intanet, abun da ya kasance wani martani mai karfi da aka mayar, game da rade-radin da ake yunkurin yadawa, cewa wai ana tilastawa al’umma aiki a sana’ar noman auduga a Xinjiang.

Ya dace kamfanonin da suke bibiyar kasashen yamma, da suke kaucema audugar Xinjiang, su tantance gaskiyar lamarin, wato kar su zama tamkar makamin siyasa da masu kyamar kasar Sin dake Amurka, da sauran kasashen yammacin duniya suke amfani da shi.

Idan wani kamfani ba ya amfani da auduga kirar Xinjiang, ba zai samu kasuwanci mai tsoka ba. A halin yanzu, yawan audugar da ake samarwa a Xinjiang ya dauki kimanin kaso 20 bisa dari, na daukacin audugar da ake samarwa a duniya, wato akwai wahalar a samu wani abun da zai maye gurbinsa.

A watan farko na bana, Amurka ta sanar da haramci na shigowa da auduga daga jihar Xinjiang, gami da dukkan kayayyakin dake amfani da audugar wurin, al’amarin da ya sanya babban matsin lamba ga masu samar da audugar Xinjiang ga manyan kamfanonin kasa da kasa. Saboda ko su nemi sabbin masu samar da auduga, ko su amince a yi musu bincike, sakamakon iri daya ne, wato kara kashe kudade.

Kamfanonin kasashen waje a kasar Sin za su dandana kudarsu idan suka gudanar da ayyukansu karkashin matsin lambar ‘yan siyasar kasashen yamma_fororder_2

A kwanan nan ma rahotanni daga jaridar New York Times sun ce, domin samun auduga, dole ne kamfanoni su saya daga jihar Xinjiang. Abu mafi muhimmanci shi ne, abun da wasu kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin suka yi, na kaucewa audugar Xinjiang, ya dagule martabarsu a kasar Sin, wannan illa ce babba kuma ta dogon lokaci a gare su.

Babu tantama, kasuwar kasar Sin na da muhimmancin gaske ga kamfanonin kasa da kasa. Musamman ganin yadda ake farfado da kasuwar kasar a bara, abun da ya baiwa wasu manyan kamfanonin samar da tufafi na kasa da kasa, damar samun farfadowa daga mawuyacin halin da suke ciki sakamakon annobar COVID-19.

Kamfanoni suna da ‘yancin zaben wurin da suke son sayen kayayyakin da suke bukata. Amma idan suka zama tamkar abun da wasu kasashe suke amfani da shi wajen kulla makircin siyasa, za su dandana kudarsu. Saboda kamfanonin su ne ke shan wahala, idan suka kaucewa audugar Xinjiang, ba wai ‘yan siyasar da suke kyamar kasar Sin ba. (Murtala Zhang)