An sayar da wani zane mai matukar girma bisa fasashin Dala miliyan 62
2021-04-01 17:33:53 CRI
Sacha Jafri, wani shahararren mai aikin zane-zane na kasar Faransa ya kwashe watanni 8 kafin ya kammala wani zane mai taken Tafiyar Dan Adam, wanda ake daukarsa a matsayin zane mafi girma a duk duniya saboda fadinsa da kusan ya yi daidai da filayen wasannin kwallon kafa guda hudu. Kwanan bayan Jafri ya sayar da zanen akan Dalar Amurka miliyan 62. Jafri ya ce, zai bayar da kudaden ga Asusun kula da yara na MDD na UNICEF da sauran kungiyoyin duniya.