logo

HAUSA

Shugaban Faransa ya ba da umarnin rufe wasu sassan kasar don dakile yaduwar COVID-19

2021-04-01 10:28:17 CRI

Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa, ya bayyana cewa, gwamnati za ta fadada matakan kullen da take dauka zuwa dukkan sassan kasar, a wani mataki na hana sake bullar annobar COVID-19 a karo na uku, za kuma a rufe makarantu na tsawon makonni uku.

Shugaba Macron wanda ya bayyana haka, cikin wani jawabi da ya yiwa ‘yan kasar ta kafar talabijin, ya ce, za a fadada dokokin da aka sanya kan sassa guda 19 da ake sanyawa ido, zuwa kasar baki daya, tun daga ranar Asabar da yamma, har na tsawon makonni hudu.

Ya ce, al’amura za su baci, idan har ba mu dauki matakin da ya dace yanzu ba. Yana mai cewa, kaso 44 cikin 100 na marasa lafiya dake fama da cutar COVID-19 dake jinya a sashen gobe da nisa, ‘yan kasa da shekaru 65 ne.

A don haka, shugaban ya ce, tun daga tsakiyar watan Afrilu, za a yiwa masu sama da shekaru 60 riga kafi. Daga ranar 15 ga watan Mayu kuma, za a fara yiwa masu tsakanin shekaru 50 zuwa 60 riga kafin. Daga tsakiyar watan Yuni kuma, za a dage batun shekaru.(Ibrahim)