logo

HAUSA

Masana: Babu yiwuwar hadarin bullar cutar COVID-19 a dakin gwajin halittu

2021-04-01 11:49:12 CRI

Masana: Babu yiwuwar hadarin bullar cutar COVID-19 a dakin gwajin halittu_fororder_20210401-bayani-Bello

Tawagar masanan kasar Sin da suka shiga aikin bincike na hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya WHO da kasar Sin suka gudanar don gano asalin cutar COVID-19, ta kira wani taron manema labaru a jiya Laraba, inda masanan suka gabatar da rahoton cewa, kusan babu yiwuwar hadarin bullar cutar COVID-19 a dakin gwajin halittu.

Kafin haka hukumar WHO ta turo wata tawagar masana da ta kunshi kasashe daban daban, wadda ta isa birnin Wuhan na kasar Sin a ranar 14 ga watan Janairun bana, inda suka kafa wata tawagar hadaka tare da wasu fitattun masanan kasar Sin, don gudanar da wani bangare na aikin binciken gano asalin cutar COVID-19, wanda ya shafi kasar Sin. Sa’an nan a taron manema labaru da aka kira a jiya, shugaban tawagar masanan kasar Sin, Mista Liang Wannian, ya ce, masanan dake cikin tawagarsu sun yi nazari kan yiwuwar bullar kwayoyin cutar ta wasu hanyoyi 4, daga bisani sun tabbatar da cewa, kusan babu yiwuwar hadarin bullar cutar a dakin gwajin halittu.

A cewar mista Liang, babu bambanci tsakanin bayanai da shaidun da masanan kasar Sin da na sauran kasashe suka gabatar, don haka dukkan mambobin tawagar hadakar sun riga sun cimma matsaya. Kana ba a kayyade hasashen da aka yi dangane da asalin cutar a wani wuri ba, saboda haka akwai bukatar gudanar da karin bincike a wurare daban daban na duniyarmu. Ya ce,

“Yadda kwayoyin cutar COVID-19 suka yadu daga dabbobi zuwa bil-Adama, har suka haddasa barkewar cutar a wata kasuwar albarkatun ruwa, ka iya daukar dogon lokaci, da shafar kaura tsakanin wurare masu nisa da juna, da aikace-aikacen tsallaka kan iyaka. Saboda haka muna bukatar sanya ido kan wurare daban daban na duniyarmu, don tara dukkan bayanan daga sassa daban daban na duniyarmu, don ci gaba da gudanar da bincike kan gano asalin cutar, da abubuwan da suka faru kafin barkewar annobar a birnin Wuhan na kasar Sin.”

A baya kafofin watsa labaru daban daban sun watsa labaru masu alaka da yadda aka gano masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasashe daban daban, tun kafin samun barkewar cutar a birnin Wuhan. Dangane da lamarin, shahararen masanin ilimin cututtuka masu yaduwa na kasar Sin, Feng Zijian, ya ce, wurin da aka fara samun barkewar wata annoba, ba dole ne ya zama wurin asalin cutar ba. Saboda haka, dukkan labarun da aka bayar suna iya zama shaidu masu muhimmanci, wadanda za su taimakawa kokarin gano dabbar da ta fara kamuwa da cutar. Feng ya ce,

“Dukkanmu mun lura da wasu rahotannin da aka watsa, cewa an gano wasu abubuwa masu dauke da kwayoyin cutar COVID-19 a sauran wurare, tun kafin barkewar cutar a Wuhan. Sai dai muna bukatar gudanar da bincike na hadin gwiwa don tantance wadannan rahotanni. Kana bayanan da muka samu za su taimakawa aikin tabbatar da lokaci da wurin da aka samu yaduwar cutar daga wata dabba zuwa wani mutum, da gano ainihin dabbar da ta fara kamuwa da cutar.”

A nasa bangare, Mista Liang Wannian ya ce, rahoton da aka gabatar dangane da binciken da aka yi don gano asalin cutar COVID-19, an wallafa shi ne bisa hakikanan bayanai da shaidu. An fara gudanar da binciken ne a kasar Sin, domin Sin ta kasance kasa ta farko da ta mika rahoton bullar cutar ga hukumar WHO. Sai dai ya kamata a ci gaba da gudanar da binciken a kasashe daban daban. Kana kwararrun da suka shiga aikin binciken sun ba da shawarwari guda 4 kamar haka:

“Da farko, a tattara bayanai a fannoni daban daban don raba wa masanan kasashe daban daban. Na biyu, a ci gaba da neman gano wadanda suka fara kamuwa da cutar a kasashe daban daban. Na uku, a kara kokarin neman gano dabbar da ka iya fara kamuwa da cutar da yada ta ga dan Adam a kasashe daban daban. Sa’an nan na hudu, a kara gudanar da bincike kan rawar da daskararran abinci ke takawa kan yaduwar cutar.”

Liang ya kara da cewa, aikin binciken gano asalin cutar na da wuya, saboda da kwayoyin cutar suna iya shiga jikin mutum a kowane wuri, a kowa ne lokaci, kana yanayin kwayoyin ya kan sauya. Amma masanan kasar Sin na son hadin gwiwa tare da abokan aikinsu na kasashe daban daban, don neman gano asalin cutar cikin sauri. (Bello Wang)

Bello