Magance kwararar hamada
2021-04-01 21:59:06 CRI
Yadda ake dukufa a kan dashe-dashen bishiyoyi ke nan a gundumar Qiemo ta jihar Xinjiang, gundumar dake iyaka da kudancin hamadar Taklimakan. Kimanin kashi biyu cikin uku na fadin gundumar Qiemo ta kasance cikin rairayi, don haka, tun daga shekarar 1998, an fara dashe-dashen bishiyoyi a wurin, kuma kawo yanzu an cimma nasarar dasa wani ziri na bishiyoyi da ke da fadin kilomita 7.5 da kuma tsawon kilomita sama da 20 a hamadar, wanda ta taimaka sosai ga kyautata muhallin zama na wurin.(Lubabatu)