logo

HAUSA

Rahoton binciken asalin cutar COVID-19 na WHO ya mari masu yada jita-jita na Amurka da kasashen yamma

2021-03-31 22:15:22 cri

Rahoton binciken asalin cutar COVID-19 na WHO ya mari masu yada jita-jita na Amurka da kasashen yamma_fororder_微信图片_20210331214122

A ranar 30 ga wata, hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a hukumance, ta fitar da rahoton binciken hadin gwiwa na Sin da WHO game da asalin cutar numfashi ta COVID-19.

Rahoton ya tabbatar da sakamakon da aka samu, a yayin taron manema labaru da tawagar hadin kan kwararrun ta shirya a Wuhan, ya kuma nuna cewa, ba zai yiwu ba ace an samu yaduwar cutar ta dakin gwaje-gwaje. Wannan dai sakamakon tamkar mari ne ga wadancan ‘yan siyasar Amurka da na kasashen yamma, wadanda suka rika yada jita-jitar cewa wai “Cutar ta bulla ne daga dakin gwaje-gwaje na Wuhan”.

Wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasashen yamma da ke adawa da kasar Sin, sun yi matsin lamba ga WHO kafin fitar da rahoton a hukumance, suna fatan WHO za ta iya biyan bukatunsu na adawa da kasar Sin.

Bayan da aka fitar da rahoton kuma, kasar Amurka ta tattara wasu kasashe kalilan don fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka nuna shakku da musanta rahoton na WHO, sannan ta kara ambatar batun cewa wai "Kasar Sin ba ta ba da hadin kai ba kan binciken", da nufin kara matsin lamba a fannin siyasa.

Lallai, a yayin da kasar Sin ke fuskantar manyan ayyukan rigakafin annobar COVID-19 a cikin kasar, ta kuma gayyaci kwararrun WHO zuwa kasar Sin har sau biyu, don gudanar da binciken gano asalin cutar, wannan ya nuna cewa, tana bude kofa, da nuna gaskiya, da kuma daukar alhaki a fannin.

Matakin da ya samu amincewa daga kwararru masu yawa na WHO, wadanda ke cewa, matsayin bude kofa da kasar Sin ke dauka ya kasance na "ba zato ba tsammani", kuma sakamakon da suka samu a ziyarar Wuhan "ya wuce hasashen da suka yi".

Binciken asalin cutar COVID-19 aiki ne na duniya duka, kuma bai kamata a kalli Wuhan kawai ba. Tuni ma aka gano mutane da suka kamu da cutar a sassa daban-daban na duniya, don haka, ya kamata a gudanar da binciken gano asalin cutar a kasashe da yankuna daban daban.

Ana sa ran cewa, kasashen da abin ya shafa za su bude kofar su, kuma bayyane su dauki nauyi kamar yadda kasar Sin ta yi, su gayyaci kwararrun WHO don gudanar da bincike game da gano asalin cutar. Musamman ma kasar Amurka wadda ta fi fama da cutar, za ta iya hada kai a fannin aikin binciken asalin cutar na duniya.

Mayar da cutar a matsayin batun siyasa ba zai iya yin nasara kan cutar ba. Ta hanyar girmama kimiyya, da hada kai ne kadai za a iya tseratar da mutane daga mawuyacin halin fama da cutar. (Bilkisu)