logo

HAUSA

Wakilin Sin ya mai da martani kan kalaman rashin gaskiya da wai wasu masanan hakkin Bil Adama suka yi dangane da kasar Sin

2021-03-31 09:19:21 CRI

Kakakin tawagar wakilin dindindin ta kasar Sin dake Geneva Liu Yuyin ya yi jawabi a jiya Litinin kan bayanan karya da wasu masana na rukunin nazarin hakkin Bil Adama da harkokin kamfanonin kasa da kasa na kwamitin kula da hakkin Bil Adama na MDD suka yi, yana mai cewa, wadannan mutanen da suka kiran kansu “masana” sun jirkita gaskiya da mai da fari baki bisa dalilai na siyasa, inda suka rika baza jita-jita cewa, wai ana tilastawa mutane yin aiki a yankin Xinjiang a gonakin tsinkar auduga, Sin ta nuna matukar rashin jin dadi da adawa kan wannan batu.

Kakakin ya nuna cewa, Sin kasa ce mai bin tsarin gurguzu, kabilu 56 suna zaune cikin hadin kai da daidaito. Gwamnatin kasar Sin na nacewa ga tunanin mai da jama’a a gaban kome cikin harkokinta. Ya zuwa karshen shekarar 2020, Sin ta kawar da matsanancin fatara a duk fadin kasar. Ban da wannan kuma, gwamnatin ta dora muhimmanci matuka kan bunkasuwar yankunan kananan kabilu. Bayanai na nuna cewa, daga shekarar 2012 zuwa 2018, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta baiwa yankin Xinjiang kudin tallafi Yuan triliyan 1.61, yawan kudin da yankin ya kashe wajen kyautata zamantakewar al’umma da samar da gubaren aikin yi da ba da ilmi da aikin jiyya da samar da gidajen kwana da sauran ayyukan cin gajiyar jama’a ya kai kashi 70%, sannan yawan kudin shiga da mazauna wurin ke samu ya rubanya sau dari tun daga shekarar 1978.

Al’ummar yankin ciki hadda ’yan kabilar Uygur suna da hakki da kuma ’yancin zabar ayyukan da suke so su yi bisa adalci, suna kuma dogara da kansu wajen jin dadin zaman rayuwarsu. Kazalika, Sin tana kan gaba a duniya wajen ba da tabbaci ga ’yancin kananan kabilu da ’yancin samun guraben aiki yi na jama’a, jita-jitar da wannan rukunin ya yada, ba shi da tushe, kuma ba za su cimma nasarar shafawa kasar Sin bakin fenti ba.

Kakakin ya ce, Sin ta dade tana amfani da na’urori na zamani don gudanar da sana’o’in samar da kayayyaki. Musamman yanzu ana amfani da injuna wajen sarrafa galibin amfanin gona da yaduna da tufafi da motoci da dai sauransu a nan kasar Sin. Alal misali, yawan audugar da aka girba da injunan zamani a Xinjiang a shekarar 2020 ya kai kashi 70%. Ban da wannan kuma, ana kokarin amfani da yanar gizo da ilmin kimiya da fasahohin zamani wajen tafiyar da sana’o’i da dama. An kuma kafa tsarin 4G a kowane kauyen kasar Sin, har ma yanzu ana kuma kokarin kafa tsarin 5G a yankunan karkara. Matakin da ya baiwa manoma ciki hadda na yankin Xinjing damar sayar da amfani gona ta Intanet.

Saboda haka, tambayar ita ce, ta yaya za a tilasta mutane yin aiki karkashin yanayin tattalin arziki na yanar gizo da amfani da na’urori na zamani? Wadannan mutanen da wai suka kira kansu “masana” ba su san kome ba kan yadda ake bunkasa fasahohin zamani da kimiya da kuma sana’o’i daban daban a kasar Sin. Babu wanda zai amince da jita-jitar da suke bazawa maras tushe.

Ban da wannan kuma, kakakin ya ce, wasu kasashen yamma sun jirkita shaidu da bayanai na gaskiya, inda suka yi karya don shafawa kasar Sin bakin fenti da tada zaune tsayi a kasar da hana bunkasuwar kasar, amma karya fure take ba ta ’ya’ya, al’ummar Sinawa ciki hadda al’ummar yankin Xinjiang, ba za su amince da su ba. Wannan rukuni ya zama mai adawa da kasar Sin, ya yi biris da bayanan da gwamnatin Sin ke gabatar masa, inda ya keta ka’idojin nuna adalci da daidaito da gaskiya da ya kamata kwamitin ya bi. Har ma’aikantansa sun fake da batun hakkin Bil Adama don bata sunan kamfanonin kasar Sin da illata zamantakewa da hakkin dan Adam na al’ummar Uygur. Shin, kwamitin ya kafa irin wannan rukuni ne don kare hakkin Bil Adama ko keta shi?

Kasar Sin na maraba da baki daga kasashen waje da su ziyarci yankin Xinjiang don ganewa idanunsu hakikanin halin da ake ciki a yankin ba tare da nuna bambancin ra’ayi ba. Sin na fatan wannan rukuni zai fahimci kuskuren da ya yi, ya kuma hanzarta gyara ra’ayin da ya dauka kan kasar Sin da inganta ayyukansa don kaucewa gabatar da bayanai da labarai na karya don cimma burinsa na siyasa. (Amina Xu)