logo

HAUSA

Kasar Sin ta cika alkawarinta na samar wa kasashen Afirka kayayyakin kandagarkin COVID-19

2021-03-31 17:49:18 CRI

Kasar Sin ta cika alkawarinta na samar wa kasashen Afirka kayayyakin kandagarkin COVID-19_fororder_1

Baya ga kasashe daban-daban da suke ci gaba da amfana da tallafin alluran riga kafin COVID-19 har ma da ma’aikatan lafiya da kayayyaki da na’urorin yaki da wannan annoba daga kasar Sin, ita ma hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin nahiyar Afirka (UNECA) ta ci gajiyar gudummawar kayayyakin lafiya na yaki da annobar COVID-19 daga kasar ta Sin. Sabanin wasu manyan kasashe da suke ci gaba da boye riga kafin annobar, a nata bangaren kasar Sin ta fita zakka, ta kuma cika alkawarin da ta yi tun farko cewa, da zarar ta gudanar da bincike aka kuma samar da riga kafin, to zai kasance na dukkan al’ummar duniya, har ma ta ce, kasashe masu tasowa ne, za su fara cin gajiyarsa,

Kayayyakin kiwon lafiyar ta kasar Sin ta samarwa hukumar, sun hada da na’urorin gwajin zafin jiki, da injunan samar da iskar oxygen, da rigunan bada kariya, da takunkumin rufe fuska da sauran kayayyakin ba da kariya ga jami’an lafiya (PPEs), wanda aka yi bikin mika su a gaban manyan jami’an hukumar ta UNECA da jami’an ofishin diflomasiyyar kasar Sin dake helkwatar hukumar ta UNECA dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a kwanakin da suka gabata.

Kasar Sin ta cika alkawarinta na samar wa kasashen Afirka kayayyakin kandagarkin COVID-19_fororder_2

Baya ga wannan hukuma, Sin tana samarwa kasashe 80, da kungiyoyin kasa da kasa 3 tallafin rigakafin COVID-19. Kazalika Sin na samarwa sama da kasashe 40 rigakafin, tana kuma hadin gwiwa da karin wasu kasashen sama da 10 a fannin binciken rigakafi, da samarwa da kuma sarrafa shi.

Masu fashin baki na bayyana irin wannan gudummawa, a matsayin wani bangare na ci gaban hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin kiwon lafiya, wanda bangarorin suka kara karfafa shi don yaki da annobar COVID-19, haka kuma wannan hadin gwiwa, wata babbar nasara ce, da ta baiwa Afirka damammakin samun kayayyakin kiwon lafiyar da take bukata don yakar annobar COVID-19 yadda ya kamata.

Kawo yanzu, kasar Sin ta samar da kayayyakin lafiya na gaggawa ga kusan dukkan kasashen Afrika da kungiyar AU. Kana hadin gwiwar Sin da Afrika wajen samar da riga-kafin annobar tana gudana kamar aka tsara.

Masharhanta na bayyana cewa, rawar da kasar Sin take takawa a fannin yaki da wannan annoba, ta kara nunawa duniya cewa, kasar tana cika dukkan alkawuran da ta yi a fannonin samar da riga kafin yaki da annobar COVID-19. Kyan alkawari aka ce cikawa. (Ibrahim Yaya)