logo

HAUSA

Adawa kasashen yamma suke da ci gaban kasar Sin ba rajin kare hakkin dan Adam ba

2021-03-30 17:38:25 CRI

Adawa kasashen yamma suke da ci gaban kasar Sin ba rajin kare hakkin dan Adam ba_fororder_微信图片_20210330172412

Yayin da Amurka da sauran kawayenta na yammacin duniya ke ci gaba da sukar kasar Sin ko zarginta da take hakkin jama’a a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, makircin Amurkar ya fito fili, domin ba rajin kare hakkin dan Adam take ba, illa dai, kokarin tauye ci gaban kasar Sin da sana’ar noman audugu dake zaman jigon tattalin arzikin jihar Xinjiang.

Kasashen yamma ciki har da Amurka da Birtaniya, na ikirarin wai ana tilastawa al’ummar Xinjiang noman auduga. Hakika noman auduga ya kasance kashin bayan tattalin arzikin jihar Xinjiang. Alkaluman hukumar kiddidiga ta kasar Sin sun nuna cewa, a bara, jihar ta samar da audugar da ta zarce ton miliyan 5, wanda ya dauki kaso 84.9 na jimilar audugar da kasar Sin ke nomawa. Haka kuma, fadin gonakin noman auduga a jihar ya kai kimanin hectar miliyan 2.54 a shekarar 2019, wanda ya dauki kaso 76 na baki daya na kasar. Don haka, jihar Xinjiang ce ke kan gaba wajen noman auduga a kasar Sin cikin shekaru 25 a jere.

Kasashen yamma na da burin siyasantar da batun noman audugar Xinjiang ta hanyar kakabawa kasar Sin takunkumai da kira da a kauracewa audugar jihar Xinjiang. Idan har da gaske manufarsu ita ce kare ’yancin al’ummar da ake tilastawa noman auduga a jihar, kamata ya yi su nemi inganta musu rayuwa ba jefa su cikin tasku ba. Idan aka kauracewa audugar da suke nomawa, an durkusar da sana’ar da suka dogara da ita wajen kyautata rayuwarsu tare da yi wa tattalin arzikin jihar mai samun armashi illa.

Bincike ya nuna cewa, saboda yadda ake samun alkhairi a lokcin tsinkar auduga na wa’adin kwanaki 50 kacal, wasu jama’ar kasar Sin da ba ’yan asalin jihar ba ma suna zuwa aikin domin kara samun kudin shiga, abun da ya nuna karara a fili cewa, ba sai an tilastawa wani aikin noma ko tsinkar auduga ba. Baya ga haka, injuna ne ke sama da kaso 90 na ayyukan da ake a gonakin.

Shin yaushe ne aikin samun na kai ya zama aikin tilas ko cin zarafi? Za a iya cewa manufar kasashen yamma ita ce, durkusar da sana’ar noman auduga da tattalin arzikin Xinjiang wanda zai haifar da koma baya ga kasar Sin. Kuma kowa ya sani cewa, idan aka rasa aikin yi, talauci ya shigo, sai kuma a shiga aikata laifuffuka, wanda kasar Sin ta dauki ingantattun matakan dakilewa.

Kasar Sin ta sha nanata cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa wajen kare cikakken iko da muradu da tsaron kasar ba, don haka, hakar wadannan masu ganin ci gaban kasar a matsayin kalubale, ba zai cimma ruwa ba. (Faeza Mustapha)