logo

HAUSA

Xi: Sin za ta taimakawa Sri Lanka domin farfadowa bayan kawo karshen annoba

2021-03-30 10:02:35 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sri Lanka don bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma samar mata da sahihan hanyoyin bunkasa tattalin arzikinta domin farfadowa bayan kawo karshen annobar COVID-19 da kuma samun dauwamamman ci gaba.

A zantawarsa ta wayar tarho da shugaban kasar Sri Lankan Gotabaya Rajapaksa, Xi ya ce, kasashen biyu sun yi hadin gwiwa wajen tabbatar da manyan ayyuka a tashar ruwan birnin Colombo da tashar ruwan Hambantota, da kuma kulla kyakkyawar hadin gwiwa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da taimako gwargwadon iyawarta da nufin taimakawa kasar Sri Lanka a yaki da annobar COVID-19, kuma sannu a hankali bangarorin biyu suna karfafa hadin gwiwarsu a fannoni kamar na zirga-zirgar jiragen sama da ba da ilmi, kana da bullo da sabbin hanyoyin karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.(Ahmad)