logo

HAUSA

Sin na kara karfafa hadin gwiwa da waje a fannin samar da makamashi

2021-03-29 11:46:26 CRFI

Sauyin yanayi kalubale ne ga daukacin bil Adama, a don haka,idam ha rana son magance wannan matsala, wajibi ne a rage yin amfani da makamashin man fetur da kwal da iskar gas, a kuma bullo da sabon tsarin samar da makamashi, wanda za a kara yin amfani da makamashin wutar lantarki da sauran makamashi masu tsabta.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta nuna kwazo da himma kan hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen waje a bangaren samar da makamashi masu tsabta ta hanyar yin amfani da fifikonta na kasuwa da fasaha.

A yayin taron kolin raya kasashen duniya na MDD da aka kira a watan Satumban shekarar 2015, kasar Sin ta gabatar da cewa, ya dace a tattauna batu bullo da wani tsarin samar da makamashi na duniya domin ingiza bukatun wutar lantarki a fadin duniya ta hanyar yin amfani da hanyar kare muhalli.

Daga baya an kafa kungiyar gudanar da hadin gwiwar makamashi tsakanin kasa da kasa a nan birnin Beijing, wadda ita ce kungiyar makamashin duniya ta farko da kasar Sin ta kafa, babban sakataren kungiyar Wu Xuan ya yi bayani cewa, bayan kokarin da aka yi a cikin shekaru biyar da suka gabata, tsarin makamashin duniya ya riga ya kasance manufar kasa da kasa, duk da cewa, a farkon kafuwarta, shawarar kasar Sin ce kawai, ana iya cewa, ta sauya daga tunani zuwa manufar ba da jagoranci kan matakin da ake dauka, yana mai cewa, “Kawo yanzu adadin mambobin kungiyar gudanar da hadin gwiwar makamashi tsakanin kasa da kasa ya kai 1157, wadanda suka kunshi kasashe da yankuna 132, ana iya cewa, kungiyar ta kasance babbar kungiyar kasa da kasa wadda ke da ta tasiri a fadin duniya, kuma a cikin shekaru biyar da suka wuce, an zabi sansanonin samar da makamashi masu tsabta sama da 200 da ayyukan da ake gudanarwa cikin hadin gwiwar tsakanin kasa da kasa fiye da 100, domin kafa babban rukuninta, a sa’i daya kuma, an yi kokari matuka domin ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashe makwabtanta a bangaren, haka kuma ta samu babban sakamako, abu mai faranta rai shi ne, an samu ci gaba wajen daidaita matsalolin karancin kudi da kasuwa da wasu kasashen dake fama da talauci suke fuskanta.”

Hakika dandalin da kasar Sin ta kafa ya hada albarkatu da kasuwa, fasahar samar da hasken wutar lantarki mai karfi da kasar Sin ke da shi, tana taka babbar rawa wajen yin cudanyar dake tsakanin bangarori daban daban a fadin duniya.

Mataimakin shugaban cibiyar yin nazari kan fasahar tattalin arziki ta kungiyar gudanar da hadin gwiwar makamashi tsakanin kasa da kasa Huang Han ya bayyana cewa, aikin hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Barzil wajen samar da wutar lantarki mai karfi (UHV) ya zama misali ga kasa da kasa wajen samar da makamashi masu tsabta tare kuma da cimma burin tsimin kudin da aka kashe, Huang Han yana mai cewa, “Fasahar da kasar Sin take da shi a fannin samar da wutar lantarki mai karfi, babban kirkire-kirkiren fasaha ne da ya kai sahun gaba a duniya, wadda ta warware matsalar samar da wutar lantarki daga wuri mai nisa, ana iya cewa, fasahar ta fi rinjaye a fannin samar da wutar lantaki a fadin duniya, kasar Sin ita ma ta samu ci gaba cikin sauri a bangaren samar da makamashi masu tsabta a cikin shekaru goma da suka gabata sakamakon fasahar.”

Kana mataimakin babban sakataren kungiyar hadin gwiwar makamashi tsakanin kasa da kasa Cheng Zhiqiang ya bayyana cewa, nan gaba kungiyar za ta ci gaba da yin kokari domin ingiza cudanyar dake tsakanin kasar Sin da kasashe makwabtanta, ta yadda za a cimma burin samar da makamashi masu inganci, tare kuma da rage iska mai dumama yanayi, a cewarsa: “Ana iya yin amfani da fasahar UHV ta kasar Sin domin jigilar wutar lantarkin da ake samarwa ta hanyar yin amfani da hasken rana da iska da ruwa daga kasar da kasashen Turai da kuma kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya zuwa kasar Sin, ta yadda za a biya bukatun kasar, a sa’i daya kuma, ana iya jigilar wutar lantarkin da ake samarwa ta hanyar yin amfani da ruwa da iska da hasken rana a kasashen dake yankin kudancin Asiya zuwa yankin dake kudu maso yammacin kasar Sin, kana akwai bukatar ingiza hadin gwiwar dake tsakanin nahiyoyin Asiya da Afirka da kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu, ko kuma tsakanin kasashen dake yankin kudancin Asiya, duk wadannan za su taimaka matuka ga yunkurin kasarmu na samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.”(Jamila)