logo

HAUSA

Ya Kamata ‘Yan Siyasar Amurka Da Na Kasashen Yamma Da Suka Bata Sunan Xinjiang Kan Batun Hakkin Bil Adama Su Waiwayi Kazantaccen Tarihinsu

2021-03-29 21:58:52 cri

Ya Kamata ‘Yan Siyasar Amurka Da Na Kasashen Yamma Da Suka Bata Sunan Xinjiang Kan Batun Hakkin Bil Adama Su Waiwayi Kazantaccen Tarihinsu_fororder_微信图片_20210329213959

"Amsar da ya kamata a bayar kan halin ko-in-kula da lafiyar musulmin kasar Sin da kasar Amurka ta yi, shi ne yin dariya, da zambo." A 'yan kwanakin da suka gabata, shafin yanar gizon RT na kasar Rasha ya nuna munafunci da shirme, na takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasar Sin kan dalilin batun hakkin dan adam a Xinjiang.

Gaskiya, wasu 'yan siyasar Amurka da na kasashen yamma sun rufe idanunsu, kan karuwar tsanantar halin wariyar launin fata a cikin kasashensu, to ko ta yaya za su damu da halin hakkin dan Adam na mutane a jihar Xinjiang ta kasar Sin? Kuma ta yaya za su yi bayani kan halin da suke ciki, wato a yayin da suke ikirarin cewa, wai suna "kulawa da" hakkin dan Adam na jama’ar Xinjiang, amma a sa’i guda kuma suna kokarin halaka sana’ar auduga ta jihar?

A halin yanzu, Amurka ita ce kasa daya tilo a duniya da ta ba da umarnin hana musulmai, tana nuna wariya da musgunawa a bayyane ga musulman dake kasar. Wani rahoto da Majalisar lura da alakar Amurka da Musulunci ta fitar a shekarar 2018 ta fitar, ya nuna cewa, yawan kungiyoyin kyamar Musulmi a Amurka, ya ninka har sau uku tun daga shekarar 2016.

Bugu da kari, kasar Amurka ta haddasa yake-yake a kasashen Afghanistan, Syria, da Iraki bisa dalilin na wai "yaki da ta'addanci," wanda ya haifar da dubun-dubatar musulmai suka rasa muhallinsu tare da hallaka iyalansu.

Ya Kamata ‘Yan Siyasar Amurka Da Na Kasashen Yamma Da Suka Bata Sunan Xinjiang Kan Batun Hakkin Bil Adama Su Waiwayi Kazantaccen Tarihinsu_fororder_微信图片_20210329214007

Irin wannan kasa ce da ke nuna rashin girmamawa ga musulmai, za ta nuna "damuwa ta musamman" ga musulman da ke jihar Xinjiang? Lallai makircinta a fannin siyasa a bayyane yake. Ainihin burinsu shi ne, bata hanyar zaman rayuwa na ma’aikatan masakar auduga na Xinjiang, da illata zaman karkon jihar, har ma da hana ci gaban kasar Sin.

Kamar yadda tsohon kanar Lawrence Wilkerson na rundunar sojan kasa ta Amurka ya taba furtawa a bainar jama'a, cewa "Batun kabilar Uygur ta Xinjiang, makirci ne da Amurka ta kitsa da nufin tayar da rikici a cikin kasar Sin, da hana bunkasuwarta".

Kaza lika shehun malami a jami'ar Harvard Steven Kelman ya yi zambo cewa, musulman da Amurka ke so kawai su ne musulmai a Xinjiang. 'Yan siyasar Amurka ba su damu da duk wata kasar Musulunci ba”.

Lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan wasan kwaikwayo game da jihar Xinjiang mai cike da karairayi da Amurka, da kasashen yamma suke yi! (Mai fassara: Bilkisu)