logo

HAUSA

An wallafa kalaman Xi game da Ilimin iyali da dabi’u

2021-03-29 09:39:57 CRI

Babbar madaba’ar wallafe-wallafe ta JKS, ta wallafa kundin bayanan Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS, game da muhimmancin iyali, da ilimin iyali da kuma dabi’u.

Littafin, wanda cibiyar nazarin tarihin jam’iyya da adadi na kwamitin koli na JKS ya harhada, ya kunshi kalamai da aka tsamo daga sama da rahotanni da jawabi da tattaunawa da sauran muhimman takardu da Xi ya gudanar tsakanin watan Nuwamban shekarar 2012 da watan Disamban shekarar 2020, kuma wannan shi ne karon farko da aka wallafa wasu daga cikinsu.(Ibrahim)