logo

HAUSA

Da zafi-zafi kan bugi karfe: Sinawa miliyan 100 sun karbi riga-kafin COVID-19

2021-03-29 15:20:52 CRI

Da zafi-zafi kan bugi karfe: Sinawa miliyan 100 sun karbi riga-kafin COVID-19_fororder_微信图片_20210329151603

Tun bayan rahoton bullar shu’umar cutar barkewar numfashi ta COVID-19 a farkon shekarar 2020, gwamnatin Sin ta yi farar dabara wajen daukar kwararan matakan kandagarkin bazuwar cutar domin dakile bazuwarta da kuma kokarin jinyar masu dauke da cutar a duk fadin kasar. Ko da yake, a hakika gwamnatin Sin da hukumomin kasar ba su yi sako-sako wajen daukar kwararan matakan dakile bazuwar cutar a kasar ba. Yayin da masanan kasa da kasa suka yi ittifakin cewa babu sauran zabin da ya ragewa duniya wajen tinkarar annobar da ya wuce samar da riga-kafin. Wannan tasa kasashen duniya da dama suka dukufa wajen ganin sun samar da riga-kafin annobar. Masu azancin magana na cewa, “da zafi-zafi kan bugi karfe”, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen samar da riga-kafin domin amfanin cikin gida da kuma sauran kasashen ketare domin a gudu tare a tsira tare. Kawo yanzu, yawan al’ummar Sinawa da aka yi musu riga kafin COVID-19 ya wuce miliyan 100. A yayin taron manema labaru da aka gudanar game da tsarin hadin gwiwar rigakafi da shawo kan annobar numfashi ta COVID-19 karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin, wanda aka gudanar a karshen wannan mako, an sanar da cewa, ya zuwa karfe 24:00 na ranar 27 ga watan Maris, yawan mutanen babban yankin kasar Sin da aka yi musu alluran rigakafin COVID-19 ya wuce miliyan 100 a duk fadin kasar.

Tun lokacin da kasar Sin ta kaddamar da tsarin bayar da rahoto na yau da kullum game da halin da ake ciki kan batun riga kafin a ranar 24 ga watan Maris, yawan mutanen da aka yi musu riga kafin ya zarce miliyan 3 a kowace rana. Koda yake dama kwamitin ko ta kwana na yaki da annobar COVID-19 na kasar ya ambata cewa, kasar Sin ta tsara gaggauta yin rigakafin, wanda kyauta ne, ta yadda daga mutane masu fuskantar barazanar saurin harbuwa da cutar, aikin zai kai ga dukkanin sassan al’ummar kasar. Da fari dai, an fara yiwa mutanen da shekarun haihuwar su ya haura 60 ne rigakafin a wasu yankuna, amma a halin yanzu za a gaggauta fadada aiki. Kaza lika za a samar da rabutattun sakwanni game da tasirin rigakafin, musamman ga wadanda ke fama da cututtuka, kamar hawan jini da ciwon suga. (Ahmad Fagam)