logo

HAUSA

Sin Tana Da Karfi Da Aniyar Mayar Da Martani Kan Matsin Lamba Da Wasu Kasashen Yammacin Duniya Suka Yi Mata

2021-03-28 16:02:34 CRI

Sin Tana Da Karfi Da Aniyar Mayar Da Martani Kan Matsin Lamba Da Wasu Kasashen Yammacin Duniya Suka Yi Mata_fororder_210328-sharhi-maryam-hoto

Kwanan baya, kasar Sin ta sanar da kakabawa wasu mutane 10, da kamfanonin Turai 4 takunkumi, sakamakon yadda suka yi matukar lahanta moriyar kasar ta Sin, kana suka yada karairayi, da farfaganda maras tushe game da kasar. Sa’an nan, ta sanar da kakabawa wasu mutane 9 da kamfanonin Burtaniya 4 takunkumi, domin maida martani kan wadannan kasashen yammacin duniya, biyo bayan takumkumin da suka kakabawa wasu mutane da kamfanonin jihar Xinjiang, bisa zargin Sin da keta hakkokin bil Adama a jihar Xinjiang, amma, matakin EU da Burtaniya ya biyo bayan karairayi, da jita jita, tare da jirkita gaskiya. Shi ya sa, kasar Sin ta dauki matakai nan take domin nuna musu cewa, duk wanda ke tsarawa da kuma yadda jita-jita, tabbas, Sin zata mayar da martani.

Al’ummomin kabilu daban daban dake sassan jihar Xinjiang suna zaman rayuwa cikin yanayin zaman karko, da tsaro, da kuma ci gaba, lamarin da ya nuna nasarar da Sin ta cimma a fannin kare hakkin dan Adam. Amma, wasu ’yan siyasa na kasashen yammacin duniya sun musanta hakikanin gaskiya a jihar Xinjiang, suna ci gaba da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin bisa hujjoji marasa tushe, domin hana bunkasuwar kasar Sin, da haddasa tashe-tashen hankula cikin gidan kasar Sin.

Amma, wadannan kasashen yammacin duniya ba zasu cimma mugun burinsu ba, sakamakon jita-jita da labaran karya da suka tsara. Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare ’yancin kan kasa, da tsaron kasa da kuma bunkasuwar kasa. Wadannan ’yan siyasan kasashen yammacin duniya ba zasu hana ci gaban kasar Sin ba, kamar yadda masu sa ido na kasa da kasa suka ce, kasar Sin, tana da karfi da aniyar maida martani ga wadanda suka matsa mata lamba. (Maryam Yang)